Matashi Ya Kashe Mahaifinsa bayan Sassara Wuyansa da Adda a Jigawa
- Rundunar 'yan sanda ta Jihar Jigawa ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da daba wa mahaifinsa adda har ya mutu a ƙaramar hukumar Gwaram
- Lamarin ya faru ne a unguwar Bakin Kasuwa da ke yankin Sara, inda ake zargin matashin mai shekaru 20 ya kai wa mahaifinsa harin da ya jawo rasuwarsa
- Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya umarci a mayar da binciken lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar (SCID) da ke babban birni Dutse
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - An kama wani matashi mai suna Muhammad Salisu, ɗan shekara 20 a jihar Jigawa bisa zargin kashe mahaifinsa.
Lamarin ya faru ne a unguwar Bakin Kasuwa a garin Sara da ke ƙaramar hukumar Gwaram, inda ake zargin ya daba wa mahaifinsa adda ya mutu har lahira.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan halin da aka shiga bayan kisar ne a cikin wani sako da kakakin 'yan sandan jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar da SP Lawan Shiisu Adam ya fitar ranar Litinin, 5 ga watan Mayu, 2025, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
Rundunar ta ce ana zargin matashin da kai wa mahaifinsa mai suna Salisu Abubakar da ke da shekaru 57 hari da adda a kafada, wuya da ƙirji, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Ana zargin matashi ya kashe mahaifinsa a Jigawa
Bayan samun rahoton faruwar lamarin, DPO na yankin Sara tare da jami’ansa suka gaggauta zuwa wurin da abin ya faru.
Sun garzaya da wanda lamarin ya ritsa da shi zuwa cibiyar lafiya ta FMC da ke Birnin Kudu domin ba shi kulawar gaggawa.
Sai dai likitan da ke bakin aiki a lokacin ya tabbatar da cewa mahaifin da aka sara da adda ya riga mu gidan gaskiya.
An kama matashin da ya kashe mahaifinsa
Bayan hakan ne aka mika gawarsa ga 'yan uwa domin gudanar da jana’iza kamar yadda addini ya tanada.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa an kama wanda ake zargi, kuma an kwato makamin da ake zargin ya yi amfani da shi wajen aikata laifin.
‘Yan sanda sun dauki matakin bincike
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Jigawa, CP AT Abdullahi, ya bada umarnin a mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka (SCID) da ke Dutse domin gudanar da cikakken bincike.
Ya ce bayan an kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu domin fuskantar hukuncin doka kamar yadda ya dace.

Asali: Facebook
Rundunar ‘yan sanda ta bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai da bayanai masu inganci domin dakile aikata laifuffuka a jihar.
An kama ango bayan mutuwar amarya a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta kama wani ango da ake zargi ya jawo mutuwar amaryarsa a jihar Jigawa.
Rahotanni sun nuna cewa an zargi angon ne da gayyatan abokan shi domin su taya shi shawo kan amaryarsa ta yi huldar aure da shi.
Legit ta rahoto cewa rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da cewa ta kama abokan angon da ake zargi an gayyace su gidan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng