Sace Mutane Ya Kai Gwamna Wuya, Ya Dakatar da Sarki kan Alaƙa da Garkuwa
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da Sarkin Uwano, George Egabor, bisa yawaitar sace mutane da kisa a masarautarsa
- Sanarwar da Kakakin Gwamna Fred Itua ya fitar ta tabbatar da dakatarwar da kuma kama Sakataren Sarkin, Peter Omiogbemhi
- An kama Omiogbemhi ne bayan wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar wani dattijo na fada mai suna John Ikhamate
- Sanarwar ta ce dakatarwar sarkin ba ta da wa'adin dawowa, kuma an dauki matakin ne don dakile matsalar tsaro a yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da babban basarake kan garkuwa da mutane da ya addabi al'ummar yankin a kwanakin nan.
Gwamna Okpebholo ya dakatar da Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a karamar hukumar Etsako ta Gabas, George Egabor nan take.

Asali: Twitter
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Fred Itua ya wallafa a shafin Facebook a yau Talata 22 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da Itua ya sanyawa hannu, ta ce an dakatar da sarkin ne saboda yawaitar sace mutane da kisa a yankin da ke karamar hukumar Etsako ta Gabas.
Gwamna ya fadi hukuncin garkuwa da mutane
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan ya dauki mataki kan masu yin garkuwa da mutane a jihar duba da yawan sace al'umma da ake yi.
Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa za a riƙa aiwatar da hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane a jihar.
Okpebholo ya nuna cewa zai sanya hannu domin aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da aikata laifin.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da aikata miyagu ayyuka a jihar ba domin ya shirya kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Asali: Facebook
An dakatar da Sarki kan garkuwa da mutane
A cewar sanarwar, jami’an tsaro sun kama Sakataren sarkin, Peter Omiogbemhi, bayan wani lamari da ya hallaka dattijon fada, John Ikhamate.
Sanarwar ta ce:
“Gwamna Okpebholo ya dakatar da Dr. George Egabor na masarautar Uwano saboda yawaitar sace mutane da kisa a yankin.
“Yanzu haka, an kama sakatarensa, Cif Peter Omiogbemhi, dangane da wani hari da ya kashe dattijo, John Ikhamate."
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an dakatar da Sarkin ba tare da wa’adin dawo da shi ba duk da cewa gwamnan yana mutunta sarakunan gargajiya.
'Yan sanda sun kama mafarauta a Edo
A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda ta Edo ta ce an cafke mafarauta hudu daga jihar Kano da makamai yayin da suka isa jihar da dare ana tsaka da rigimar kisan Hausawa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Moses Yamu, ya bayyana cewa an kama mafarauta ne ba Fulani makiyaya ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sadarwa.
Sunayen mafarautan da aka kama sun hada da Yusuf Abdulkarim, Mujaheed Garba, Shittu Idris sai Jamilu Habibu, kuma duk daga Doguwa a Kano suka fito.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng