An Kona Gidaje, Rumbunan Abinci a Sabon Rikici tsakanin Tiv da Jukun a Taraba
- Wasu da ake zargin Jukunawa ne sun kai hari garin Dekeh da ke kan hanyar Wukari–Kente, suka kone gidaje 15 tare da harbin wani dan kauyen
- Rikicin da ya faru da misalin karfe 1:00 na dare ya sake tayar da hankali a tsakanin al’ummomin Tiv da Jukun masu takun-sakar filaye a Taraba
- Rundunar ‘yan sanda da sojoji sun kai dauki cikin gaggawa, aka ceto wanda aka harba, yayin da aka fara bincike da zaman sulhu don dakile karin rikici
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - A wani sabon rikici da ya afku tsakanin al’ummomin Jukun da Tiv a jihar Taraba, an kai hari a garin Dekeh da ke kan hanyar Wukari zuwa Kente.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kona gidaje 15 tare da barin wani mutum da raunin harbin bindiga.

Asali: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru da misalin karfe 1:00 na daren Talata, kuma ya jefa al’umma cikin halin dar-dar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa maharan kusan shida ne, dauke da bindigogi, suka bude wuta ba tare da kakkautawa ba kafin su fara cinna wuta a gidan mutane da rumbunan abinci.
An kona gidaje da kayan abinci a Taraba
Baya ga gidajen da aka kona, maharan sun kuma lalata kayan abinci, musamman irin doya, da dama mallakar manoma a garin.
Wani mazaunin kauyen mai suna Mdue Saaondo ya samu raunin harbin bindiga a harin, jami’an tsaro suka ceto shi cikin gaggawa suka garzaya da shi Asibitin Jami’ar Wukari.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kai dauki a kan lokaci, ta ce tuni aka fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata mummunar ta’asar.
Ana kokarin sulhu tsakanin Tiv da Jukun
Rikici tsakanin Jukun da Tiv dai na da dogon tarihi, musamman kan batun mallakar fili da iyakokin kauyuka a yankin kudancin Taraba.
Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa ana ci gaba da sa ido da sintiri a yankin domin hana sake aukuwar wani hari ko rikici.

Asali: Facebook
Jami’an tsaro sun fara daukar mataki
Haka kuma ana shirin gudanar da zaman sulhu tsakanin shugabannin gargajiya na Wukari da bangarorin da rikicin ya shafa domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
A cewar hukumomi, tuni aka fara wani shiri na tsaurara tsaro a yankin tare da shirya zaman tattaunawa tsakanin al’ummomin Jukun da Tiv.
Rundunar ‘yan sanda ta ce za a karfafa sintiri da kai dauki cikin gaggawa domin hana kara tabarbarewar tsaro da rikice-rikice a yankin, musamman da ake fuskantar damina.
Legit ta tattauna da Isa Muhammad
Yayin tattaunawa da wani mazaunin jihar Taraba, Isa Muhammad, ya bayyanawa Legit cewa rikicin Jukun da Tiv yana da sarkakiya sosai.
Isa Muhammad ya ce:
"Akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan da suka kamata idan ana son shawo kan rikicin, an dauki matakai da dama a baya amma har yau ba a daina rikicin ba.
'Hakan yana nuna akwai wata matsala a kan matakan da ake dauka. Ya kamata gwamnati ta sake nazari sosai."
'Yan bindiga sun kai wani hari jihar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara dauke da makamai sun kai sabon hari kauyukan jihar Filato.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai harin ne cikin dare a lokacin da mutane suke barci a karamar hukumar Barikin Ladi.
Shugaban karamar hukumar Barikin Ladi ya tabbatar da faruwar harin tare da bayyana cewa an yi jana'izar wadanda suka mutu a harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng