Kisan ’Yan Sanda a Delta: An Kame Mutum da Ake Zargi da Yiwa Jami’ai Kisan Gilla

Kisan ’Yan Sanda a Delta: An Kame Mutum da Ake Zargi da Yiwa Jami’ai Kisan Gilla

  • Rundunar 'yan sanda ta yi nasarar kame wadanda ake zargi da kashe jami'anta a jihar Delta kwanakin baya
  • A baya, an hallaka wasu jami'an 'yan sanda a yayin da suke bakin aiki, lamarin da ya daga hankalin kasa baki daya
  • Ba wannan ne karon farko da 'yan ta'adda ke yiwa sojoji ko 'yan sanda kisan gilla ba, hakan ya sha faruwa a baya

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a kisan jami’anta a yankin Ughelli da ke jihar Delta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin Jihar Plateau: Fulani na zargin sojojin Najeriya da yi masu bakin aika-aikata

Ya ce an kashe jami’an ne da ke bakin aiki a ranar 23 ga watan Fabrairu, inda aka yi musu kwanton bauna da ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda shida.

An kame makasan 'yan sanda a Delta
An kama wadanda suka kashe 'yan sanda a Delta | Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai ga kamen 'yan ta'addan Delta

Adejobi ya ce kamen ya biyo bayan wani gagarumin bincike da jami’an ‘yan sandan suka yi, rahoton Daily Trust.

A cewarsa, da fari an cafke mutane biyar da ake zargi da laifin jim kadan bayan faruwar lamarin yayin da aka kama wasu karin uku a wurare daban-daban.

Ya ce kama karin ukun ya biyo bayan bayanai da da hadin kan da wadanda aka kama da farin suka bayar.

A ina aka ajiye 'yan ta'addan da suka kashe 'yan sanda?

Adejobi ya ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda, inda suke taimakawa wajen gudanar da bincike tare da kai wa ga kame sauran masu laifin, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babu hannu na a kashe sojojin Najeriya, Sarkin Delta da ya mika kansa ga 'yan sanda

Ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dukufa wajen ganin an kama duk wadanda ke da hannu wajen aikata kisan kai da sauran ayyukan ta'addanci makamantansu tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Kakakin ‘yan sandan ya kuma ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, tare da kwararan hujjoji da zarar an kammala bincike.

Yadda aka kashe jami'ai a Delta

A tun farko, rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da rasa jami’anta guda shida a wani aikin samar da zaman lafiya a jihar Delta.

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, ta nuna cewa jami’an sun rasa ransu ne a wani harin kwanton bauna da 'yan bindiga suka kai musu a dajin Ohoro na jihar Delta.

'Yan sandan dai suna bincike ne a dajin kan ɓacewar wasu abokan aikinsu guda uku lokacin da lamarin ya auku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel