Gwamna Bago da Jerin Shugabannin Najeriya da za a Karrama a London
- Za a karrama wasu fitattun shugabannin Najeriya a bikin bayar da lambar yabo na Triangle Face of Africa da za a gudanar a birnin London na Burtaniya
- Gwamna Sanwo-Olu, Wole Olanipekun, Tunji-Ojo, Tahir Monguno da wasu ‘yan siyasa da jiga-jigan gwamnati za su kasance cikin wadanda za a karrama
- Otunba Olufemi Salako ya bayyana cewa za a karrama wasu masu hangen nesa da suka taka rawar gani wajen kawo cigaba da canza rayuwar al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A ranar Asabar, 10 ga Mayu, 2025, birnin London da ke Birtaniya zai kasance cike da manyan baki daga kasashen Afrika.
Hakan za ta faru ne saboda gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta Triangle Face of Africa Leadership.

Asali: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa taron da kamfanin Triangle News International ke shiryawa zai gudana da misalin karfe 12:00 na rana a dakin taro na RHB 300 a jami’ar Goldsmiths.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’in kamfanin Triangle, Otunba Olufemi Salako ya ce za a yi taro ne domin girmama shugabanni masu nagarta da suka nuna kwarewa, gaskiya da kyakkyawan shugabanci a Afrika.
Shugabannin Najeriya za su hallara London
Daga cikin fitattun ‘yan Najeriya da za su karbi lambobin yabo akwai Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya, Wole Olanipekun SAN.
Haka kuma, za a karrama Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo; Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago da Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Punch ta wallafa cewa sauran wadanda za a karrama sun hada da dan shugaban kasa, Seyi Tinubu; Ministan Matasa, Ayodele Olawande Wisdom.

Asali: Facebook
Sauran sun hada da shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa; da Sanata Mohammed Tahir Monguno wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Arewa.
Bayan haka, akwai wasu fitattun ‘yan majalisar dattawa irin su Orji Uzor Kalu da Eteng Jonah Williams, da kuma jami’in harkokin sadarwa na NNPC, Femi Soneye.
Tasirin taron ga kasashen Afrika
Otunba Salako ya ce taron na da nasaba da tunawa da tarihin Afrika da kuma raya al'adun nahiyar.
A cewar Salako:
“Wannan ba kawai karramawa ba ce, illa dai nuna girmamawa ga Afrika da kuma masu bada gudummawa wajen canja rayuwar al’umma ta hanyar shugabanci.”
Ya kara da cewa taron na bana zai ba da dama ta musamman da za a hada shugabannin siyasa, kasuwanci da kungiyoyin fararen hula domin tattauna hanyoyin inganta cigaban Afrika.
Ana sa ran taron zai kara karfafa zumunci da hadin gwiwa tsakanin ‘yan Afrika da ke gida da mazauna kasashen waje, musamman a fannin shugabanci, tattalin arziki da ci gaban al’umma.
Legit ta tattauna da Lawan Musa
Wani matashi mai harkar siyasa a jihar Bauchi, Lawal Musa ya bayyana wa Legit cewa bai kamata shugabanni su shagala da karbar lambar girma ba a yanzu.
Malam Lawal ya ce:
"Kowa ya san matsalolin da muke fama da su a kasar nan. Me zai sa wani shugaba ya shagala da karbar lambar yabo a halin da ake ciki?"
'Ko da ba su suka nemi a karrama su ba ya kamata su sani cewa a halin da kasar ke ciki babu wani da yake bukatar a karrama shi saboda shugabanci na gari."
An kama tsohon sojan Birtaniya a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Birtaniya ta nesanta kanta da wani mutum da aka kama bisa zargin safarar makamai a Najeriya.
An kama mutumin ne a filin jirgin sama a jihar Legas yana kokarin tafiya Birtaniya bayan kama wasu makamai da aka ce suna da alaka da shi.
Birtaniya ta ce mutumin ya taba aiki da rundunar sojinta a baya, amma an dade da sallamar shi kuma ba shi da alaka da ita a yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng