Jerin Sunaye: Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Kafa Sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya

Jerin Sunaye: Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Kafa Sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa sababbin jami'o'i na kuɗi guda 11 domin bunkasa harkokin neman ilimi a Najeriya
  • Shugaban hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa, Farfesa Abdullahi Ribaɗu ne ya miƙa lasisin fara aiki ga sababbin makarantun a Abuja yau Laraba
  • Ministan ilimi, Tunji Alausa ya buƙaci makarantun kudi su yi haɗin guiwa da juna da haɗa kai da jami'o'in duniya wajen bunƙasa harkokin ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta miƙa lasisin gudanarwa ga sababbin jami’o’in kudi guda 11 da gwamnatin tarayya ta amince da su kwanan nan.

Shugaban NUC, Farfesa Abdullahi Ribadu, shi ne ya miƙa lasisin fara aiki ga wakilan sababbin jami'o'in a Abuja ranar Laraba.

Hukumar NUC.
Gwamnatin Tarayya Ta ba sababbin Jami'o'i 11 lasisin fara aiki a Najeriya Hoto: @uncosnaija
Asali: Twitter

Ya jaddada muhimmancin jami’o’in kudi wajen tallafawa makarantun gwamnati, musamman ba matasa da ke neman ilimi a Najeriya guraben karatu, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamnati ta ba jami'o'in kudi lasisi

Farfesa Abdullahi Ribadu ya ce tun bayan bude damar kafa jami’o’i masu zaman kansu a shekarar 1999, an samu gagarumar ci gaba a fagen ilimi.

Ya ce:

“A 1999 muna da jami’o’i 49 kacal, inda 23 daga cikinsu suka kasance na kudi amma yanzu Najeriya na da jami’o’i 298, daga ciki kuwa 159 (kimanin kaso 53.3%) na kuɗi ne."

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, wanda ya halarci taron ba jami'o'in lasisi, ya bayyana cewa sababbin jami’o’in za su bada damar samun ilimi mai inganci a matakin gaba da sakandare.

A cewarsa wannan mataki wani bangare ne na shirin farfaɗo da harkar ilimi a Najeriya, inda aka fi mai da hankali kan fannonin kimiyya, fasaha, injiniya, lissafi da likitanci (STEMM).

“Najeriya tana da dimbin masu digiri a fannin zamantakewa. Abin da muke bukata yanzu su ne masu basira da dabaru na warware matsaloli, wadanda za su iya gina masana’antu, tituna da inganta rayuwa,” in ji Alausa.

Tunji Alausa.
Ministan ilimi ya koka kan yadda jami'o'in kudi ke gaza cika ƙa'ida Hoto: @DrTunjiAlausa
Asali: Twitter

Matsalar da ake fuskanta daga jami'o'in kudi

Ya kara da cewa da yawa daga cikin jami’o’in kudi da aka kafa a baya ba sa cika ka’idar inganci da ake bukata, cewar rahoton Vanguard.

Don magance hakan, ministan ya ce NUC tana ƙoƙarin gyara tsarin tabbatar da ingancin dukkan jami’o’i, na gwamnati da na kudi, su zama cibiyoyin koyarwa na gaskiya.

Ya kuma bukaci jami’o’in kudi da su yi hadin gwiwa da junansu tare da ƙulla alaƙa da jami’o’in ƙasashen waje, domin Najeriya na da damar zama cibiyar haɗin gwiwar ilimi ta duniya.

Sababbin jami’o’in da aka ba lasisi

1. New City University, Aiyetoro, Jihar Ogun

2. Lens University, Ilemona, Jihar Kwara

3. Kevin Ezeh University, Mgbowo, Jihar Enugu

4. Monarch University, Iyesi Ota, Jihar Ogun

5. Tonnie Iredia University of Communication, Benin, Jihar Edo

6. Isaac Balami University of Aeronautic and Management, Jihar Lagos

7. Eranova University, Kuje, Babban Birnin Tarayya (FCT)

8. Southern Atlantic University, Uyo, Jihar Akwa Ibom

9. University of Fortune, Igbotako, Jihar Ondo

10. Minaret University, Ikirun, Jihar Osun

11. Abdulrasaq Abubakar Toyin University, Ganmo, Jihar Kwara.

Gwamnati za ta ɗauki ma'aikata a makarantu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta shirya ɗaukar sababbin ma'aikata a jami'o'i, kwalejojin fasaha da na ilimi a faɗin Najeriya.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya umarci dukkan manyan makarantu tarayya da aka ba su izinin daukar ma’aikata su yi tallar guraben da suke nema.

Wannan mataki yana da nufin tabbatar da gaskiya, buɗaɗɗen tsarin daukar aiki , da kuma bai wa dukkan ’yan Najeriya da suka cancanta damar neman aiki cikin adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262