Ministan Tinubu Ya Ji Koken Jama'a, Ana Tsoron Kudirin Haraji zai Ruguza TETFund

Ministan Tinubu Ya Ji Koken Jama'a, Ana Tsoron Kudirin Haraji zai Ruguza TETFund

  • Ma’aikatar ilimi ta Najeriya ta bayyana cewa ana yin garambawul ga kudirin haraji domin tabbatar da TETFund ba zai daina samun kudi ba
  • Idan ba a yi gyaran kafin amince wa da kudirin haraji ba, za a rage kaso na kudin da TETFund ke samu daga haraji tun daga 2025 har zuwa 2029
  • Sannan daga shekarar 2030 shirin ba zai sake samun wani kaso ba, wanda masana ke ikirarin cewa zai rugurguza TETFund baki daya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMa’aikatar ilimi ta Najeriya ta bayyana cewa ana yin garambawul ga kudirorin gyaran haraji da gwamnatin tarayya ta gabatar.

Ya ce an dauki matakin gyaran ne domin tabbatar da dorewar asusun tallafa wa ilimin manyan makarantu (TETFund) har zuwa bayan shekarar 2030.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

TETFUND
Ministan ilimi ya ce kudirin haraji zai iya cutar da TETFund Hoto: ochukwu Michael Ozioko/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Ministan ilimi, Tunji Alausa, ya bayyanawa manema labarai a Abuja a ranar Alhamis cewa ana shirin gyara tsarin haraji da zai shafi fannin ilimi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Oktoba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika wa majalisar dokoki ta kasa wasu kudirori hudu na gyaran haraji domin tantancewa da amincewa.

Yadda kudirin harajin Tinubu zai shafi TETFund

Solacebase ta ruwaito cewa, wani bangare na kudirin gyaran harajin da aka gabatar ya na nufin rushe harajin ilimi da kuma maye gurbinsa da sabon tsarin.

Idan aka aiwatar da sabon tsari, zai shafi yadda TETFund ke samun kudi, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen gina kayayyakin more rayuwa a manyan makarantun gwamnati.

Sabon tsarin zai fara ne daga 2025/2026, inda za a bukaci duk wasu kamfanonin da ake biyan haraji su biya 4%, sannan daga 2027 zuwa 2029 kudin zai ragu zuwa 3%.

A karkashin wannan kudiri, 50% na kudin da aka tara daga harajin zai shiga asusun TETFund a 2025 da 2026.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta zauna kan kudirin harajin Tinubu kafin amincewa da shi

Haraji: TETFund za ta daina samun kudi daga 2030

Daga shekarar 2027 zuwa 2029, 66% na kudin harajin ci gaban kasa zai shiga asusun TETFund. Amma daga shekarar 2030, hukumar za ta daina samun wani kaso daga kudin gaba daya.

Tinubu
Shugaba Tinubu ya aika dokar kudirin gyaran haraji ga majalisa a shekarar 2024 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Daga wannan lokaci, harajin ci gaban kasa zai koma 2% kawai, wanda za a yi amfani da shi domin tallafa wa shirin rancen dalibai na gwamnatin tarayya.

Sai dai wannan mataki ya fuskanci suka daga masana da sauran masu ruwa da tsaki, wadanda suka yi zargin cewa hakan yunkuri ne na ruguje TETFund.

"Za a gyara kudirin haraji" Inji Minista

Yayin taron manema labarai, ministan ilimi, Tunji Alausa ya ce makomar TETFund za ta shiga mawuyacin hali idan aka amince da kudirin haraji.

Ya bayyana cewa ma’aikatar ilimi tana aiki tare da kwamitin gyaran haraji na majalisar dokoki domin kare asusun kudin TETFund.

A cewarsa:

"Kun ji labarin sababbin dokokin haraji da ake shirin aiwatarwa, wanda ke nuna cewa za a kawo karshen TETFund, NASENI, da NITDA nan da shekarar 2030. Amma mun zauna da kwamitin haraji na majalisa."

Kara karanta wannan

"Jonathan ya yi bankwana da siyasa," PDP ta magantu kan fito da shi takara

"Zan iya tabbatar muku da cewa hakan ba zai faru ba. TETFund zai ci gaba da wanzuwa har abada. Majalisa da bangaren zartarwa suna aiki a kan gyaran dokokin harajin."
"Da zarar an kammala kudirin, za a ci gaba da ware kudaden harajin da ake ware wa TETFund har ma da NITDA da NASENI.

Majalisa ta na duba kudirin harajin Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa Majalisar wakilai za ta fara nazarin rahotannin kudirin gyaran haraji da kwamitin sauraron ra'ayoyin jama'a ya tattaro kafin a kai ga amince wa da shi.

Shugaban majalisa, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya bukaci ‘yan majalisa da su halarci zaman ranar Alhamis domin su taka rawarsu wajen tantance rahoton da kuma karɓarsa a hukumance.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng