Abu Ya Girma: Gwamnatin Tarayya Ta Shiga Batun Hutun Azumi a Makarantun Arewa
- Gwamnatin Tarayya ta na tattaunawa da jihohin Bauchi, Katsina, Kebbi da Kano kan bude makarantun da aka rufe saboda Ramadan
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ministar Ilimi ta ce rufe makarantun na tsawon wata guda zai haddasa asarar lokaci ga dalibai
- Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatocin jihohi suka ki karban korafin kungiyar CAN da ta ce rufe makarantun zai kawo koma baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bukaci gwamnatocin jihohin Bauchi, Katsina, Kebbi da Kano da su sake duba shawarar da suka yanke na rufe makarantu saboda azumin Ramadan.
Gwamnatocin jihohin sun rufe makarantun ne domin ba dalibai da malamai damar yin ibada cikin nitsuwa a azumi.

Asali: Facebook
Ministar Ilimi, Dr. Suwaiba Ahmad ce ta bayyana bukatar bude makarantun a wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin din Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suwaiba Ahmad ta ce rufe makarantun na tsawon kusan wata guda zai rage wa dalibai damarmakin karatu, tare da haddasa tsaiko ga tsarin ilimi.
Gwamnatin tarayya na tattaunawa da jihohi
Ministar ilimi, Suwaiba Ahmad ta ce duk da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da ikon tilasta wa jihohi bude makarantun su, ta fara tattaunawa da su don su sake duba wannan mataki.
Suwaiba Ahmad ta ce:
"Muna kokarin ganin cewa an bude wadannan makarantun domin kada dalibai su rasa damarmakin karatu.
"Mun fahimci cewa kowace jiha na da 'yancinta a fannin ilimi, amma ya na da kyau a dauki matakan da za su fi dacewa da ci gaban kasa."
A cewar Ministar, matakin rufe makarantun na iya haddasa cikas ga shirin Gwamnatin Tarayya na bunkasa ilimi da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Dambarwar jihohi da kungiyar CAN
Tun a farko dai kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta ce rufe makarantun a jihohin Arewa a dalilin Ramadan abu ne da zai haifar da matsala ga ilimi.
Sai dai duk da haka, gwamnatocin jihohin sun ce ba gudu ba ja da baya a kan matakin da suka dauka na ba dalibai hutu.
Gwamnatocin jihohin sun ce ba kawai rana daya su ka tashi suka yanke hukunci ba, sai da aka tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.
Wane mataki jihohi za su dauka kan lamarin?
Matakin rufe makarantun na ci gaba da haddasa muhawara tsakanin malamai, iyaye da kungiyoyin farar hula.
Wasu na ganin cewa ya kamata jihohin su samar da mafita da ba za ta hana dalibai karatu ba yayin azumi, maimakon rufe makarantu gaba daya.
A halin yanzu, ana jiran matakin da gwamnatocin jihohin Bauchi, Katsina, Kebbi da Kano za su dauka bayan tattaunawa da Gwamnatin Tarayya.

Asali: Facebook
Ramadan: An rage lokutan aiki a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta rage lokacin aiki ga ma'aikatan jihar saboda fara azumin watan Ramadan.
Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi ya bayyana cewa ya dauki matakin ne domin ba mutane damar yin ibada yadda ya kamata a azumi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng