'Yan Bindiga Sun Kai Hari Benue, Sun Halaka Mace Mai Juna 2 da Wasu Mutane 10

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Benue, Sun Halaka Mace Mai Juna 2 da Wasu Mutane 10

  • Akalla mutane 11 ne 'yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai kauyen Ole’Adag’aklo da ke gundumar Usha a jihar Benue
  • Shugaban karamar hukumar Agatu, Yakubu Ochepo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce 'yan bindigar sun tafi da wasu
  • Ko da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Benue, SP Catherine Anene, ta ce ba a sanar da ita faruwar lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Benue - A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane 11 ciki har da wata mata mai juna biyu a kauyen Ole’Adag’aklo da ke gundumar Usha, a karamar hukumar Agatu ta jihar Benue.

Kara karanta wannan

Aiki ba lasisi: Kotu ta yanke hukuncin dauri kan 'yan canji 17 da aka kama a Kano

'Yan bindiga kai hari kauyen jihar Benue
'Yan bindiga sun kashe akalla mutane 11 a harin da suka kai jihar Benue. Hoto: @frhyacinthalia
Asali: Facebook

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da yamma inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, wanda ya kai ga ajalin mutane 11 tare da sace wasu.

'Yan bindiga sun sace mutane" - Ochepo

Shugaban Agatu, Yakubu Ochepo, wanda ya tabbatar wa da Jaridar Daily Trust faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Litinin, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An kashe mutane 11. Mun gano gawar mace mai juna biyu, dattijo da matasa biyar. Sojoji kuma sun yi nasarar gano sauran gawarwakin mutane hudun.
"A yanzu haka ina Makurdi domin kai rahoto ga dakarun soji na Operation Whirl Stroke (OPWS). Lallai muna bukatar dauki domin sun sace wasu mutanen."

Jaridar SaharaReporters ta ruwaito kakakin ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce ba a sanar da ita labarin faruwar lamarin ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Aliero sun tafka barna, sun hallaka sojoji, jikkata wasu 11 a Katsina

'Yan bindiga sun kai hari jami'ar Kogi

A wani labari, mun ruwaito maku yadda wasu ‘yan bindiga suka kai hari a jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence (CUSTECH), Osara, da ke Okene a jihar Kogi, tare da yin garkuwa da dalibai.

Majiyoyin tsaro sun shaidawa manema labarai cewa dalibai na cikin ajujuwa suna karatun jarabawar jarabawar zangon farko a lokacin da 'yan bindigar suka kai farmakin.

An ce ‘yan bindigar sun shiga ajujuwa ne a ranar Alhamis da daddare kuma sun yi harbe-harbe tare da yin awon gaba da dalibai akalla 25.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel