An Kwato Bindigar Harbo Jirgin Sama wajen 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno

An Kwato Bindigar Harbo Jirgin Sama wajen 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno

  • Mayakan CJTF da ke aiki da rundunar Operation Hadin Kai sun dakile harin 'yan ta'adda a garin Izge, Gwoza dake jihar Borno
  • Sun kashe mayakan ISWAP guda uku tare da kwato bindigar harbo jirgin sama da babura uku da 'yan ta'addan ke amfani da su
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa babu asarar rayuka daga bangaren fararen hula yayin harin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Mayakan rundunar sa-kai ta CJTF da ke aiki a karkashin Operation Hadin Kai sun yi nasarar dakile wani hari daga mayakan ISWAP.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan CJTF sun samu nasarar ne a garin Izge da ke karamar hukumar Gwoza, jihar Borno.

Boko Haram sun sha kashi
'Yan CJTF sun kwato makamai wajen Boko Haram. Hoto: @DefenceHQ
Asali: Getty Images

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne a daren Talata yayin da 'yan ta'addan suka yi yunkurin kutsa kai cikin garin a boye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani shaidan gani da ido ya ce jami’an sa-kai na CJTF sun yi artabu da mayakan ISWAP na tsawon lokaci kafin su tilasta musu guduwa.

An kwato bindigar harbo jirgi a Borno

Rahoto ya bayyana cewa CJTF sun yi tsayuwar daka sun fatattaki 'yan ta'addan ISWAP, suka kashe uku daga cikinsu yayin musayar wuta mai tsanani.

Shaidar gani da ido ya ce:

“Mayakan CJTF sun yi nasarar hana shigowar 'yan ta'addan. Sun kashe uku daga cikinsu, sauran kuma sun tsere da raunuka zuwa dazuka,”

Baya ga hakan, an kwato bindiga da ake aiki da ita wajen harbo jirgi da kuma babura guda uku da 'yan ta'addan ke amfani da su wajen kai hari.

Majiyar ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rayukan fararen hula ba, kuma yanzu an dawo da zaman lafiya a garin Izge.

Zulum
An dakile harin Boko Haram a jihar Borno. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

CJTF na taka rawa a yankin Arewa maso Gabas

Rundunar CJTF na daga cikin manyan ginshikan da ke taimaka wa sojojin Najeriya wajen yaki da ta’addanci musamman a Arewa maso Gabas.

Bayan taimako wajen tattara bayanan sirri, CJTF na taka muhimmiyar rawa wajen kare al’ummomi daga hare-haren 'yan ta'adda.

Tuni dai jami’an tsaro suka kara sanya ido a yankin domin hana sake faruwar irin wannan hari, yayin da aka ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa.

Jama’ar yankin sun bayyana godiya ga jajircewar CJTF da kuma sauran jami’an tsaro bisa yadda suka dakile harin ba tare da asarar rayuka ba.

An kashe mutane 6 a sabon harin Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai sabon hari karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun kai harin ne tsakar dare a lokacin da mutanen yankin suke cikin barci.

Mutanen garin da aka kai wa harin sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane shida tare da jikkata da dama da aka kai su asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng