'Ba Hausawa ba ne': Gwamna Ya Fayyace Komai, Ya Fadi Masu Kashe Mutane a Benue

'Ba Hausawa ba ne': Gwamna Ya Fayyace Komai, Ya Fadi Masu Kashe Mutane a Benue

  • Gwamna Hyacinth Alia ya yi ikirarin cewa ‘yan ta’addan da yanzu ke kai hare-hare a garuruwan jihar Benue ba ‘yan Najeriya ba ne
  • Ya ce yaren da suke magana da shi ya sha bamban da na Hausawa, Yarbawa ko Fulani, kuma sun fi kama da ‘yan ƙasashen waje
  • Gwamnan ya ce rahotanni sun nuna cewa maharan na da mafaka a Taraba, Nasarawa da Kamaru, kuma akwai tsari a kai hare-harensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamna Hyacinth Alia, ya bayyana cewa masu kai hare-hare a garuruwan jihar Benue ba asalin 'yan Najeriya ba ne.

Ya ce 'yan ta'addar suna amfani da bindigar AK-47 da AK-49, kuma suna magana da baƙon yare da ba a saba ji ba, sannan ba sa kama da 'yan Najeriya.

Gwamna Hyacinth Alia ya yi magana kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Benue
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

Gwamna Alia ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na Channels TV a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Alia ya fadi masu kai hari Benue

Hare-haren da 'yan ta'adda suka kai Benue ya shafi garuruwa da dama, sannan mutane da yawa sun rasa rayuka tare da tilasta wa wasu barin gidajensu.

Da aka tambaye shi ko ya san wadanda ke kai hare-haren, Gwamna Alia ya ce abu na farko shi ne a fahimci irin barazanar da ke akwai a kasa.

Gwamnan ya ce:

“Mun san Fulani, Yarbawa, da Hausawa ta fuskar harshe da kamanni. Amma waɗannan ba su kama da ko daya daga cikin ukun nan.
“Suna farmakar mutane da manyan makamai. Hausar da suke yi ba irin Hausarmu ba ce, kuma kamanninsu ya nuna cewa ba ‘yan Najeriya ba ne.”

"Ba Hausawa ko Fulani ba ne" - Gwamna Alia

Gwamna Alia ya ce rahotannin bayanan sirri daga mazauna yankunan sun nuna cewa waɗanda ke kai hare-haren 'yan ƙasashen waje ne.

Ya ce:

“Wani lokaci su na cewa maharan 'yan Mali ne. Yarensu ba kamar irin na Fulani ko Hausa da mu ke dasu a Najeriya ba ne. Su ba 'yan kasar nan ba ne.”

Gwamnan ya bayyana cewa wannan sabon salo ne na ta'addanci da ya fi haɗari fiye da rikicin da aka saba gani na makiyayan cikin gida.

“Da farko dai muna da yakin makiyaya ne ke kai hare-haren. Mun riga da mun karance su. Amma wannan sabon nau’in hare-hare ne da ya fi na makiyaya muni."

- Gwamna Alia.

Gwamnan Benue, ya yi magana kan hare-haren 'yan bindiga a jihar
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Twitter

"Akwai tsari a hare-harensu" - Gwamnan Benue

Gwamnan jihar na Benu ya bayyana cewa yadda ake kai hare-haren na nuni da cewa akwai tsari da shiri mai zurfi a lamarin.

Ya bayyana cewa:

“A yadda ake shirya kisan, ya nuna cewa abu ne da aka tsara cikin kwarewa. Ai wasu kananan hukumomin Benue na da iyaka da Kamaru.”

Alia ya bayyana damuwa kan yadda aka bar iyakokin a buɗe wanda a cewarsa ke zama hanya mafi sauƙi ta shigowar 'yan ta'adda daga ƙasashen waje.

“Rahotanni na nuna cewa 'yan ta'addar na da mafaka a wasu yankunan Taraba, Nasarawa da kuma cikin kasar Kamaru.”

- Gwamna Alia.

Alia ya ce 'yan bindiga sun mamaye Benue

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Hyacinth Alia ya nuna damuwa matuƙa kan tabarbarewar tsaro a Benue, musamman yayin da damina ke gab da kamawa.

Ya zargi 'yan ta'adda da ƙoƙarin korar mutane daga ƙauyukansu don mamaye matsugunansu, inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta kawo agaji da gaggawa.

Gwamnan ya ja kunnen ‘yan siyasa masu cin moriyar rikicin, yana mai cewa duk wanda aka kama da hannu a lamarin, za a fallasa shi a bainar jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.