Bayin Allah da Yawa Sun Mutu Yayin da Ƴan Bindiga Suka Buɗe wa jama'a wuta a jihar Arewa

Bayin Allah da Yawa Sun Mutu Yayin da Ƴan Bindiga Suka Buɗe wa jama'a wuta a jihar Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai mummunan hari kan mutane a wani ƙauye da ke karamar hukumar Apa a jihar Benuwai ranar Alhamis
  • Rahoto ya nuna cewa ana fargabar maharan sun kashe mutane da yawa lokacin da suka bude wuta kan mai uwa da wabi kan mazauna kauyen
  • Har kawo yanzu ba a tantance yawan mutanen da suka mutu ba kuma babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Wasu miyagun ƴan bindiga da ake zaton fulani makiyaya ne sun kai mummunan farmaki kan jama'a a ƙauyen Adijah, ƙaramar hukumar Apa a jihar Benuwai.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ana fargabar ƴan bindigan sun kashe bayin Allah da dama a harin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Yan bindiga sun kai hari a jihar Benue.
Rayuwa da yawa sun salwanta yayin da ƴan bindiga suka kai hari a Benue Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Lamarin wanda ya afku da yammacin ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, ya tilasta wa mazauna kauyen guduwa daga gidajen su zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya faru

An tattaro cewa maharan sun kutsa kai cikin ƙauyen wanda ke da nisan kilomita ƙalilan da titin Otukpo-Oweto, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Bsyanai sun nuna cewa sun kashe bayin Allah masu ɗumbin yawa da har yanzun ba a gama tantance adadinsu ba kawo yanzu.

Har yanzu da muke haɗa muku wannan rahoto ba a gano yawan mutane da suka rasa rayukansu ba a harin. Babu sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda.

Legit Hausa ta fahimci cewa wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a sassan Najeriya musamman a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Ƴan kasuwa sun rage farashin kayan masarufi, talakawa zasu samu sauƙin sayen abinci

A makonnan, wasu tsagerun ƴan bindiga sun kashe rayuka cikin harda jami'in tsaro kana suka yi awon gaba da nutane akalla 40 a jihar Zamfara.

Yan bindiga sun yi ajalin lauya

A wani rahoton kuma Wasu ƴan bindiga da ba a sani ba sun halaka Barista Victor Onwubiko, a kan hanyarsa ta komawa jami'ar jihar Abia daga mahaifarsa da ke Imo.

Rahotanni sun bayyana cewa lauyan ya rasa ransa ne ranar Asabar da daddare a kan titin Okigwe zuwa Oturu, wanda ake yawan kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel