Yadda Tinubu, Atiku, Shettima da Ribadu Suka Yi Sallar Idin Layya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da sallar Idi a jihar Legas tare da manyan jam'iyyar APC da NSA, Malam Nuhu Ribadu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi sallar Idi a Masallacin AYA da ke Abuja tare da kira ga hadin kai da zaman lafiya
- Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bukaci ‘yan Najeriya su nuna dattako da hakuri yayin da ya yi sallar Idi a Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yau Laraba, 27 ga watan Mayun 2026 al'ummar Musulmi ke gudanar da bikin babbar sallar layya a Najeriya da fadin duniya.
Shugabannin Najeriya da masu ruwa da tsaki sun gudanar da sallar Idin layya a jihohi daban-daban tare da sauran jama'ar da suke wakilta.

Source: Facebook
Tinubu ya yi sallar Idi a Legas
Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya wallafa a X cewa Bola Tinubu ya gudanar da sallar Idi tare da dimbin al'ummar Musulmi a yau Laraba.
Shugaba Tinubu da tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Raji Fashola, dan takarar gwamna na APC a Legas da sauran Musulmai sun gudanar da sallar Idi a Dodan Barracks da ke jihar Legas.
An kuma ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, a filin idi yana zaune kusa da Tinubu.
Atiku ya yi sallar Idi Abuja
A daya bangaren kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tawagar shi sun gudanar da sallar Idi a birnin tarayya Abuja.
A wani sako da ya wallafa a Facebook, Atiku ya ce:
“Na hadu da sauran Musulmai da safiyar yau a Masallacin AYA da ke Abuja domin gudanar da sallar Idi tare da gode wa Allah bisa ni’imominsa marasa iyaka.
“Yayin da muke bikin wannan lokaci mai tsarki, ina addu’ar Allah ya kara karfafa hadin kai, tausayi, sadaukarwa da zaman lafiya a matsayinmu na al’umma daya kasa daya.
“Barka da Sallah ga dukkan Musulmai a Najeriya da ma duniya baki daya. Allah ya karbi ibadunmu tare da ba kasarmu zaman lafiya mai dorewa da wadata.”

Source: Facebook
Shettima ya yi Idi a Borno
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya je Ramat Square da ke Maiduguri a jihar Borno domin gudanar da sallar Idin layya na shekara-shekara.
Hadimin Shettima, Stanley Nkwocha ya wallafa a X cewa mataimakin shugaban kasar ya ce:
“Sakonmu ga ‘yan Najeriya shi ne su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkan ‘yan kasa. Kuma yayin da muke shiga yanayin siyasa, akwai bukatar nuna dattako, hakuri da kuma kyakkyawar mu’amala a siyasar mu,”
Ga bidiyon yadda Shettima ya isa filin Idi:
Alhajin Najeriya ya rasu ranar sallah
A wani labarin, mun kawo muku cewa yayin da ake cigaba da bukukuwan sallar layya, wani dan Najeriya ya rasu a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan
Atiku ya lallasa yan takara 2, ya samu nasara a zaben fitar da gwanin ADC a Sakkwato
Duk da cewa hukumomi ba su fadi sunan mutumin ba, an samu rahotannin da suka nuna ya fito ne daga jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.
Wasu daga cikin mahajjatan Najeriya a Saudiyya sun bayyana cewa mutumin ya rasu ne ranar Laraba bayan kammala hawan Arafa a ranar Talata.
Asali: Legit.ng

