Bayan Ya Ƙi Barin PDP, an Taso Gwamna Dauda a Gaba kan Dokar Ta Ɓaci a Zamfara
- NDYC ta bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci a Zamfara saboda yawaitar kashe-kashe da tabarbarewar tsaro da doka
- Kungiyar ta ce lamarin ya kai matakin da ake rasa tsaro kwata-kwata, mazauna yankin ke rayuwa cikin tsoro da fargabar rasa rayuka
- Sannan kungiyar NDYC ta jaddada cewa tun da aka ayyana dokar ta baci a Jihar Rivers, ya kamata a yi gaggawa a yi irinsa a Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yenagoa, Bayelsa - Kungiyar 'Niger Delta Youth Congress' (NDYC) ta tura bukata ga gwamnatin tarayya kan jihar Zamfara.
Kungiyar ta bukaci ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda yawaitar tashin hankali da rashin tsaro.

Asali: Twitter
Zamfara: An roki Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci
A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Israel Uwejeyan, ya sanya wa hannu, NDYC ta ce satar mutane da kashe-kashe sun yi kamari, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta kwatanta lamarin da yadda gwamnatin tarayya ta hanzarta ayyana dokar ta baci a jihar Rivers, inda ta ce ya dace a Zamfara.
NDYC ta ce rikicin da ke faruwa a jihar Zamfara yana barazana ne ga rayuwar jama’a, inda al’ummomi ke zaune cikin tsananin tsoro.
Kungiyar ta bayyana cewa murabus da tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, MD Abubakar, ya yi daga hukumar tsaron jihar ya nuna gazawar gwamnati.

Asali: Facebook
Dalilan neman sanya dokar ta-ɓaci a Zamfara
Har ila yau, NDYC ta ce akwai rikici na siyasa a jihar, majalisar dokokin jihar ta rabu gida biyu, kuma ana rikici tsakanin ‘yan majalisa.
NDYC ta ce idan ana ganin rikicin siyasa ya sa aka ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers, to, rikicin Zamfara ya fi cancanta a dauki matakin.
Kungiyar ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Tsaro ta kasa da su gaggauta ayyana dokar ta baci a Zamfara ba tare da bata lokaci ba.
Sanarwar ta ce:
“Muna rokon Shugaban kasa da Majalisar Tsaro ta kasa da su ayyana dokar ta baci a Zamfara ba tare da bata lokaci ba.
"Irin gaggawar da aka nuna a jihar Rivers ya kamata a nuna ita ma a Zamfara, kasa da haka nuna wariya ne.
"Muna tare da duk ‘yan Najeriya da ke fuskantar rashin tsaro ko a Arewa, Kudu, Gabas ko Yamma. Amma muna bukatar adalci.
Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda ake nuna bambanci inda ake fifita wasu yankunan fiye da wasu a Najeriya.
Ƙungiyar ta ce:
"Niger Delta ba za ta amince a ci gaba da nuna bambanci ba, inda wasu yankuna ake fifitasu, wasu kuma ana nunawa karfi."
An bukaci Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Zamfara
Kun ji cewa wata ƙungiyar Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda tabarbarewar tsaro.
Kungiyar CAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da mulkin kama karya yayin da ta ce jihar ba ta samun wani ci gaba a yanzu.
NCAJ ta ce garuruwa sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga, jami’an gwamnatin jihar na amfana da haramtacciyar hakar ma’adinai.
Asali: Legit.ng