Amurka Ta Kama 'Yan Najeriya 22 da ke Amfani da Hotunan Batsa wajen Damfara

Amurka Ta Kama 'Yan Najeriya 22 da ke Amfani da Hotunan Batsa wajen Damfara

  • Hukumar FBI ta Amurka ta cafke ’yan Najeriya 22 da ake zargi da hannu a zamba ta intanet wacce ta haddasa mutuwar fiye da matasa 20
  • An gudanar da samamen ne karkashin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin Najeriya, Amurka, Kanada, Ostiraliya da Birtaniya
  • FBI ta ce ana amfani da bayanan da aka kama a wayoyin da aka kwace wajen ci gaba da bincike da kuma bankado sauran masu laifi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A wani samamen kasa da kasa, hukumar FBI ta sanar da kama wasu ’yan Najeriya 22 da ake zargi da hannu a zamba ta intanet wacce ta jawo mutuwar matasa da dama.

An gudanar da samamen ne karkashin Operation Artemis, inda hukumomin Najeriya, Amurka, Kanada, Ostiraliya da Birtaniya suka haɗa kai wajen zakulo wadanda ke da hannu a lamarin.

Amurka
Amurka ta kama 'yan Najeriya da ake zargi da damfara. Hoto: Bayo Onanuga|Donald Trump
Asali: Facebook

A cewar rahoton Vanguard, binciken da aka gudanar cikin kusan shekaru biyu ya gano yadda masu aikata laifin ke amfani da kafafen sada zumunta wajen yaudarar matasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan damfarar na samun hotunan tsiraicin matasa a fadin duniya, sannan su yi amfani da su wajen tsoratar da su da kuma karɓar kudi.

'Yan damfara na amfani da hotunan batsa

Binciken ya nuna cewa wadanda ake zargin suna fakewa a matsayin matan da ke son abokanta a intanet domin samun damar karɓar hotunan batsa daga matasan.

Bayan samun hotunan, suna fara barazanar fallasa su idan ba su biya wani adadin kudi ba, kuma ko bayan biyan kudin, barazanar kan ci gaba har zuwa kai ga matasan su dauki rayukansu.

Wata jami’ar FBI, Karen R., ta bayyana cewa wannan laifi ba wai kawai damfara ba ne, illa ce kai tsaye ga rayuwar matasa masu tasowa.

Gudumawar EFCC da hukumomin kasashe

A shekarar 2023, FBI da jami’an 'yan sanda na Kanada da Ostiraliya sun kafa sansanin wucin gadi a Legas tare da haɗin gwiwar hukumar EFCC domin samame.

Punch ta wallafa cewa kwamandan EFCC, Michael Wetkas, ya ce fahimtar yanayin Najeriya ya taimaka matuƙa wajen nasarar samamen.

Wayoyin da aka kwace daga hannun wadanda ake zargin sun bayyana hujjojin bayanai da hotuna da suka gamsar da cewa sun aikata laifin.

Amurka
Jami'an FBI za su cigaba da farautar 'yan damfara a Najeriya. Hoto: Getty Image
Asali: UGC

Sakon gargaɗi da cigaba da bincike

Hukumomin Amurka sun ce samamen ya aika gagarumin sako ga matasa da ke neman shiga harkar damfara ta intanet cewa dubunsu za ta cika a kwana a tashi.

Michael Ervin daga ofishin jakadancin Amurka a Legas ya bayyana cewa za su ci gaba da bincike da kuma nemo sauran wadanda ba a kama ba.

Amurka ta bukaci fitar da bayanan sirrin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta bukaci a fitar da wasu takardu da suka shafi shugaba Bola Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa takardun da ake bukata a bayyana sun shafi safarar kayan maye da ake zargin shugaban da hannu a ciki.

Tun a lokacin da Bola Tinubu ya fara maganar takarar 2023 'yan hamayya suka yawaita bayanai kan takardun da ake rike da su a Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng