'Yan Ta'adda Sun Kutsa Gidan Basarake da Bindigogi, Sun Sace Matarsa da 'Yarsa
- 'Yan bindiga sun afka gidan Hakimin Aboro, Alhaji Shuaibu Suleiman Galadima, inda suka sace matarsa Harira da 'yarsa Maryam
- Lamarin ya jefa al’umma cikin firgici, yayin da yunkurin ceto wadanda aka sace ya jawo mutuwar wani matashi da kuma jikkata wani
- Mazauna garin sun roƙi gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin ceto wadanda aka sace da kuma kare lafiyar al’umma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Wasu 'yan bindiga sun sace Harira Abdullahi, matar Hakimin Aboro da ke ƙaramar hukumar Sanga a Jihar Kaduna, tare da 'yarsa Maryam Suleiman Galadima.
Rahotanni sun nuna cewa hakan ya faru ne a wani hari da 'yan ta'addan suka kai gidan hakimin da yammacin Lahadi.

Asali: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa 'yan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 7:36 na yamma, suka kutsa gidan hakimin suka yi awon gaba da matarsa da 'yarsa ba tare da wata barazana ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin garin da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar Litinin, yana mai cewa al’ummar garin sun shiga firgici bayan faruwar harin.
An kashe masu kokarin ceto matar basaraken
Business Day ta wallafa cewa bayan jin labarin sace matan, mazauna garin sun haɗu domin bin 'yan bindigar cikin daji da nufin ceto su, amma hakan ya haifar da mummunar asara.
Wani mazaunin garin ya ce:
"Mun bi su cikin daji, amma sai suka buɗe mana wuta. Muna cikin hakan ne suka harbe ɗaya daga cikinmu, Umar Abdullahi, har lahira.
"Sannan suka jikkata wani Suleiman wanda yanzu haka yana jinya a asibiti,"
Majiyar ta ce an birne mamacin bisa koyarwar Musulunci, kana ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara zage dantse wajen ganin an ceto matan da aka sace.
Halin da ake ciki bayan sace matar basarake
A cewar mazauna yankin, harin ya bar al’umma cikin damuwa da fargaba, inda suka bukaci ƙarin jami’an tsaro a yankin domin hana sake aukuwar irin harin.
Sun bayyana cewa satar mutane don neman kudin fansa na ƙara ta’azzara a yankunan karkara na Jihar Kaduna, musamman a ƙananan hukumomi kamar Sanga da Kagarko.

Asali: Twitter
Rundunar ƴan sanda ba ta ce uffan ba
Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna bai yi nasara ba, domin mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aike masa ba.
A halin da ake ciki, al’umma na ci gaba da fatan samun sauƙin lamarin, tare da roƙon Allah da jami’an tsaro su kai ga ceto Harira da Maryam lafiya.
'Yan ta'adda sun kai hari jihar Borno
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda da ake tunanin 'yan Boko Haram ne sun kai wani mummunan hari jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a yankin Chibok a lokacin da ake jana'izar wani mutum da ya rasu.
Baya ga haka, maharan sun kashe mutane akalla 15 tare da sace wasu da ba su ji ba, ba su gani ba da kuma kona gidaje da coci.
Asali: Legit.ng