Abin Fashewa da Ake Zargin Bam ne Ya Tarwatse a Borno, Sama da Mutane 25 Sun Mutu
- Wani abin fashewa da ya tarwatse ya hallaka matafiya da dama a kusa da kauyen Furunduma, kan hanyar Kala-Balge zuwa Gamboru-Ngala
- ‘Yan sanda a jihar Borno sun ce mutane 26 sun mutu, ciki har da maza, mata da yara, yayin da wasu uku suka tsira da raunuka masu muni
- Gwamna Babagana Zulum ya bayyana damuwa kan dawowar Boko Haram a Tafkin Chadi da dajin Sambisa, duk da karɓar tubabbu 300,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya tarwatse tare da kashe matafiya masu yawa a kan hanyar Kala-Balge zuwa karamar hukumar Gamboru-Ngala a jihar Borno.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, lokacin da wata mota daga Rann, hedikwatar Kala-Balge, ta taka bam din da 'yan ta'adda suka dasa a kan hanyar.

Asali: Original
"Mutane 26 bam ya kashe a Borno" - 'Yan sanda
Kakakin rundunar ‘yan sandan Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch, yana mai cewa wadanda suka jikkata na kwance a asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ASP Nahum Daso ya ce:
“A yau (Litinin) da misalin karfe 12 na rana, wata mota kirar Isuzu mai lamba Xa265kku daga yankin Kala Balge zuwa Gamboru Ngala ta taka IED a kusa da kauyen Furunduma. Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane 26 ciki akwai maza 16, mata 4 da yara 6.”
Ya kara da cewa direban motar da wasu mutum biyu sun tsira, amma sun samu munanan raunuka, yayin da aka garzaya da su asibiti domin ceto rayukansu.
Wani harin bam ya kashe fasinjoji 8 a Borno
Sai dai kuma, wasu majiyoyi daga yankin sun ce mutane 8 ne kawai suka mutu, yayin da da dama suka samu munanan raunuka.
Wata majiya daga yankin ta shaidawa jaridar cewa, “Mata da yara na cikin wadanda suka mutu. Kimanin mutane takwas ne suka mutu.”
Lamarin ya faru ne kwanaki 16 bayan wani bam ya hallaka fasinjoji takwas tare da jikkata wasu 11 a hanyar Maiduguri–Damboa a jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ASP Daso ya ce wadanda suka jikkata na ci gaba da samun kulawar likitoci a asibiti, inji rahoton SaharaReporters.

Asali: Facebook
Zulum ya koka kan dawowar Boko Haram
Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki uku da Gwamna Babagana Zulum ya ce mutane 300,000 da suka ce sun tuba daga kungiyar Boko Haram aka karɓa cikin shekara uku da suka gabata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ministan tsaro, Badaru Abubakar; babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa; da wasu manyan kwamandojin soji suka kai ziyara Maiduguri.
Zulum ya taba bayyana cewa Boko Haram na sake taruwa a yankunan Tumbuns na tafkin Chadi da tsaunukan Mandara a cikin dajin Sambisa.
Ya ce yayin da sojojin Najeriya ke amfani da karfi wajen fatattakar su, akwai bukatar ayi amfani da hanyoyin sulhu wadanda suma na da matukar amfani a yaki da ta'addanci.
Bam ya tarwatse da 'yan sanda a jihar Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Wani abin fashewa da ake zargin nakiya ce ya tarwatse da motar ‘yan sandan Najeriya a kan titin Maiduguri-Damaturu, jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Kuturu, inda jami’an rundunar RRS ke gudanar da sintiri, kafin su taka 'bam' din da ake zargin ISWAP ta dasa.
A wani hari dabam a jihar Kogi, wasu ‘yan bindiga sun kashe yara shida a dajin Ogbe yayin da suke kiwon dabbobi, abin da ya tayar da hankulan jama’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng