Wani Abin Fashewa Ya Tarwatse da Jami'an 'Yan Sandan Najeriya a Jihar Borno

Wani Abin Fashewa Ya Tarwatse da Jami'an 'Yan Sandan Najeriya a Jihar Borno

  • Wani abin fashewa da ake zargin nakiya ce ya tarwatse da jami’an ‘yan sandan Najeriya uku a kan titin Maiduguri-Damaturu a Borno
  • Ana zargin ‘yan ta’addan ISWAP ne suka dasa nakiyar da ta jikkata jami’an RRS yayin da suke sintiri a kusa da Garin Kuturu da ke jihar
  • A wani hari dabam, ‘yan bindiga sun kashe yara shida a dajin Ogbe, Kogi, yayin da suke kiwo, lamarin da ya janyo fargaba ga mazauna yankin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Rahotanni daga jihar Borno na nuni da cewa wani abin fashewa da ake zargin nakiya ne ya tarwatse da jami'an 'yan sandan Najeriya.

An ruwaito cewa jami'an 'yan sandan uku sun samu munanan raunuka bayan nakiyar ta tarwatse da su, a kan titin Maiduguri-Damaturu da ke jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka

Ana fargabar nakiya ta tarwatse da jami'an 'yan sanda a jihar Borno
Borno: 'Yan sanda uku sun jikkata da nakiya ta tarwatse a kan titin Maiduguri-Damaturu. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Borno: Abin fashewa ya tarwatse da 'yan sanda

Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da ya fitar ya nuna cewa ana zargin 'yan ta'addan kungiyar ISWAP ne suka dasa wannan nakiya da ta tashi da jami'an 'yan sandan.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana a kusa da kauyen Garin Kuturu, tsakanin Auno da Jakana.

Nakiyar ta tashi ne lokacin da jami’an ‘yan sandan rundunar Rapid Response Squad (RRS) ke sintiri, lamarin da ya lalata motarsu.

An garzaya da jami'an 'yan sanda asibiti

Rahotanni sun ce fashewar ta haddasa wawakeken rami mai zurfin kafa uku da faɗin kafa biyar a wurin da abin ya faru.

A cewar rahoton, tawagar kwararrun jami’an ‘yan sanda masu tarwatsa bama-bamai (EOD-CBRN) sun isa wurin don bincike amma ba a samu wata nakiya ta biyu ba.

Kara karanta wannan

'Dan sandan Najeriya ya sha giya ya bugu, ya harbe wani mutumi har lahira

Bayan tabbatar da yankin a matsayin mai tsaro, an sake bude hanya domin masu amfani da titin su ci gaba da zorga-zirga, sai kuma ga wannan abu da ya faru.

An ce yanzu haka jami’an ‘yan sanda da suka jikkata suna samun kulawa a asibitin kwararru na jihar Borno kafin a sallame su.

‘Yan bindiga sun kashe yara 6 a jihar Kogi

'Yan bindiga sun kashe yara shida a jihar Kogi
'Yan bindiga sun farmaki yara suna kiwo a Kogi, an kashe shida. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Fashewar nakiyar a Borno na zuwa ne yayin da wasu‘yan bindiga suka kashe yara shida a dajin Ogbe da ke jihar Kogi.

Rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa harin ya faru ne a ranar Lahadi, inda ‘yan bindigar suka kai wa yaran hari a lokacin da suke kiwo.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun dira sansanin da ake kiwon dabbobin, inda suka bude wuta kan yaran tare da kashe su har lahira.

Iyalan mamatan sun kai rahoton afkuwar lamarin ga ‘yan sanda a ranar 11 ga watan Maris, 2025, kamar yadda rahoton ya nuna.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kai hari Borno, sun yi barna kafin isowar sojoji

Jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin, inda suka dauki hotunan gawarwakin da suka fara rubewa, tare da fara bincike kan harin.

'Yan ta'adda sun farmaki sojoji a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan ta’adda sun sake aikata ta’asa bayan kashe manoma 40 a Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya.

An ce 'yan ta'addan sun yi wa sojoji da fararen hula kwantan bauna a lokacin da suka je dauko gawarwakin manoman da aka kashe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng