'Bam' da Ƴan Ta'adda Suka Dasa Ya Halaka Bayin Allah Sama da 10 a Arewacin Najeriya

'Bam' da Ƴan Ta'adda Suka Dasa Ya Halaka Bayin Allah Sama da 10 a Arewacin Najeriya

  • Mutane da dama sun mutu yayin da bam da ya tashi da wata motar bas a titin Baga zuwa Kukawa a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno
  • Sahihan bayanai sun nuna cewa aƙalla mutum 10 suka mutu yayin da wasu 20 suka ji raunuka kuma galibi sun zo wucewa ne
  • Ana zargin mayakan kungiyar ISWAP ne suka dasa bam ɗin da nufin kashe sojoji amma bisa tsautsayi motar haya ta bi ta kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Ana fargabar akalla mutane 10 sun mutu sakamakon tashin wani bam da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka dasa a titin Baga-Kukawa a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar bas ta haya ta taka Bam ɗin kuma ya tashi, bayan mutanen da suka mutu, wasu kusan 20 sun ji raunuka daban-daban.

Kara karanta wannan

"Lamarin ya yi muni" Ƴan bindiga sun kewaye gari guda, sun tafka mummunar ɓarna a Kaduna

Sojojin Najeriya.
Mutane sun mutu yayin bam ya tashi da wata motar bas a jihar Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Wata majiya mai tushe daga sashin tattara bayanan sirri na sojoji ta tabbatar da faruwar lamarin ga Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin ƴan tada kayar baya a yankin tafkin Chadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta shaidawa Makama cewa cewa bam ɗin ya tashi da motar ne ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, 2024.

Yadda bam din ya tashi a Borno

Makama ya wallafa a shafinsa na manhajar X cewa bam ɗin ya hallaka fasinjoji 10, yayin da wasu mutum 20 suka jikkata kuma.an garzaya da su asibiti.

"Motar ta yi bindiga a lokacin da ta taka bam, fasinjoji 10 suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata," in ji shi.

Duk da Zagazola Makama ya rahoto cewa mutum 10 suka mutu amma wasu majiyoyi masu ƙarfi sun tabbatar wa jaridar Punch cewa aƙalla 16 ne suka mutu.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya ragu a wasu gidajen mai yayin da Dala ta ƙara karyewa a Najeriya

Kakakin rundunar sojoji ta bakwai, Laftanar Kanal Ajemusu Jingina, ya ce:

"Ba zan iya cewa komai ba saboda lamarin ya faru ne a wurin da ke karkashin kulawar rundunar sojojin haɗin guiwa mai hedkwata a Ndjamena a Chadi."

Mutum 16 bam ya kashe a Borno

Wani mazaunin garin Baga, Bukar Wakil, ya bayyana cewa sun ji ƙarar tashin bam kuma aƙalla mutane 16 suka rasa rayukansu.

Ya ce:

"Mun samu labarin an dasa bam din ne da nufin ɗana wa sojoji tarko, amma kafin su zo wata motar haya ta taka, aƙalla mutum 16 suka mutu wasu 20 suka raunata galibi masu wucewa."

An sace mutane a Kaduna

Wasu rahotanni daga Kaduna sun nuna cewa ƴan bindiga sun kai kazamin hari kauyen Angwar Danko da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Wakilin yankin a majalisar dokokin jihar, Yahaya Ɗan Salio, ya ce ya samu labarin har yanzun ƴan ta'addan ba su bar kauyen ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel