'Yan Bindiga Sun Kai Hari cikin Dare a Sokoto, an tafka barna
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Miyagun ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Illela-Baraya a ƙaramar hukumar Gwadabawa a daren ranar Juma'a, 25 ga watan Afrilun 2025
- A yayin harin da aka kai a ƙauyen, sun hallaka mutum uku bayan sun buɗe wuta kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Illela-Baraya da ke cikin ƙaramar hukumar Gwadabawa a jihar Sokoto.
Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a daren ranar Juma'a, 25 ga watan Afirilun 2025, sun kashe mutane uku yayin da suke harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Asali: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan, waɗanda suka zo da yawa, sun kai harin ne da misalin karfe 10:00 na dare.
A lokacin harin, sun harbe wasu mutane uku, suka yi musu munanan raunuka waɗanda daga bisani suka rasa rayukansu.
Jami'an tsaro sun fatattaki ƴan bindiga
Daga samun labarin aukuwar harin, jami’an tsaro sun garzaya zuwa wurin da abin ya faru da gaggawa.
Sun yi fafatawa da ƴan bindigan inda suka fatattake su har suka tsere ba tare da samun nasarar sace dabbobi ko wani abu ba.
Sai dai, duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi wajen kai agaji da kuma kawo ceto cikin gaggawa, mutanen da suka ji rauni sun ce ga garinku nan, yayin da likitoci suka tabbatar da mutuwarsu bayan an kai su asibiti.
Bincike da aka gudanar a wurin da aka kai harin ya gano harsashi guda uku na bindiga ƙirar AK-47, wanda ke nuna irin bindigar da ƴan bindigan suka yi amfani da ita wajen harbe-harben.

Asali: Twitter
Bayan haka, dakarun tsaro sun ci gaba da sintiri a ƙauyen da kewaye, suna gudanar da bincike na musamman don tabbatar da cewa babu sauran barazana daga wajen ƴan bindiga, da kuma tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar yankin baki ɗaya.
A ƙarshe, hukumomin tsaro sun bayyana cewa za su ƙara ƙaimi wajen tura ƙarin jami’ai da kuma ƙara sa ido a yankunan karkara da ke fama da matsalolin tsaro, domin hana sake aukuwar irin wannan farmaki a gaba.
Abin da ƴan sanda suka ce kan harin
Legit Hausa ta samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai wanda ya tabbatar da aukuwar harin.
"Eh sun shiga ƙauyen a daren Juma'a, inda suka harbi mutum uku waɗanda suka riga mu gidan gaskiya."
"Jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakarsu bayan an gwabza faɗa."
- DSP Ahmad Rufai
Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Maru.
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka aƙalla mutane 28 da ba su ji ba, ba su gani ba a farmakin da suka kai a ƙauyukan.
Daga cikin mutanen da ƴan bindigan suka kashe har da masu haƙar ma'adanai waɗanda ke neman na abinci lokacin da aka buɗe musu wuta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng