Da Gaske ne 'Yan Bindiga Sun Dafa Naman Mutane a Tukunya?

Da Gaske ne 'Yan Bindiga Sun Dafa Naman Mutane a Tukunya?

  • Bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta da ke nuna wasu mutane suna girki a manyan tukwane a fili ya jawo zargin cewa 'yan bindiga ne ke dafa naman mutane
  • Bincike ya tabbatar da cewa bidiyon ba ya da alaƙa da 'yan bindiga, illa dai an ɗauke shi ne a wani bikin auren Fulani a ƙaramar hukumar Shongom da ke jihar Gombe
  • Mai bidiyon ya bayyana cewa an sauya masa ma'ana ne a kafafen sada zumunta, yana mai tabbatar da cewa an yi girkin ne a wajen bikin auren 'yan uwansa biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe – Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta da ke nuna wasu mutane suna girki da manyan tukwane a wani fili, ya haddasa ce-ce-ku-ce bayan wasu suka yi iƙirarin cewa 'yan bindiga ne ke dafa naman mutane.

Kara karanta wannan

Kai mutane Hajji, taimakon almajirai da ayyukan Peter Obi a Arewa

Sai dai binciken da cibiyar tantance gaskiyar labarai ta Dubawa ta gudanar ya gano cewa wannan iƙirari ba gaskiya ba ne, domin bidiyon an ɗauke shi ne a wani bikin auren gargajiya na Fulani a jihar Gombe.

'Yan bindiga da wajen da ake dafa abinci
'Yan bindiga a hagu da wajen da ake dafa abinci a dama. Hoto: @pcfjbl|@ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Dubawa ta rahoto cewa bidiyon ya samu dubban kallon masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka yaɗa shi tare da zargin cewa naman mutane ne ake dafawa.

Yadda bidiyon ya bazu

Wasu masu amfani da X sun yi iƙirarin cewa bidiyon ya nuna 'yan bindiga suna dafa naman mutanen da suka yi garkuwa da su.

Wani mai amfani da X mai suna @pcfjbl ya rubuta a X cewa:

"Na ga wani bidiyo a TikTok da ke nuna 'yan bindiga suna dafa naman mutane a manyan tukwane bakwai."

Sai dai wasu sun yi shakku kan wannan zargi, inda wani mai suna Ade ya tambaya:

"Wa ya tabbatar muku cewa naman mutane ne? Kuma ta yaya kuka tabbatar cewa 'yan bindiga ne?"

A Facebook ma, wasu sun sake wallafa bidiyon tare da irin wannan zargi, lamarin da ya sa Dubawa ta fara bincike domin gano gaskiyar abin da ke ciki.

Kara karanta wannan

Fitaccen mai barkwanci a Najeriya, AY ya daina zuwa coci, ya fadi abin da ya faru

Abin da bincike ya gano

An yi bincike da na'urori domin gano asalin bidiyon, amma ba ta samu wata hujjar da ke nuna cewa bidiyon ya shafi 'yan bindiga ko dafa naman mutane ba.

Daga bisani, an gano cewa asalin bidiyon ya fito ne daga wani asusun TikTok mai suna @ahmadumuhammed463, wanda aka wallafa ba tare da wani bayani da ke danganta shi da ta'addanci ba.

Mai asusun, Muhammad Ahmadu wanda aka fi sani da Gombawa, ya shaida ta wayar tarho cewa bidiyon an ɗauke shi ne yayin bikin auren ƙannensa biyu, Adamu Musa da Ahmadu Musa, a ƙauyen Fandi Kara Lalaipido da ke Shongom a jihar Gombe.

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya bayyana cewa an gudanar da ɗaurin auren ne ranar 31 ga Janairu, 2026, yayin da aka yi girkin da ke cikin bidiyon washegari a matsayin wani ɓangare na shagulgulan bikin.

Gombawa ya kuma ba da bidiyo 17 da suka nuna yadda aka yanka shanu, aka shirya abinci da sauran abubuwan da suka gudana a bikin, inda aka tabbatar cewa bidiyon da ya bazu wani ɓangare ne kawai na cikakken faifan bikin.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya kayyade sadakin zawarawa zuwa N1,500 a Bauchi? Gaskiya ta fito

Baya ga haka, an lura cewa babu wata alama a cikin bidiyon da ke nuna cewa mutanen 'yan bindiga ne ko kuma suna dafa naman mutane.

Ga bidiyon bogin da aka yada a X a kasa:

An kashe sojan a Nasarawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta ƙaryata rahotannin da suka ce an kashe wani jami'in leƙen asirin soja, Kanal Abdussalam A. Ude, a cikin Abuja.

Rundunar ta bayyana cewa bincikenta ya gano lamarin ya faru ne a Badna da ke ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa, ba a cikin Abuja ba kamar yadda wasu kafafen sada zumunta suka yaɗa.

'Yan sandan sun yi kira ga kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa domin kauce wa yaɗa bayanan ƙarya da ke haifar da fargaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng