Yan Ta'adda Sun Daƙile Jigilar Mutane a Garuruwa bayan Lalata Gada da Harin Bam
- Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun ta da bam a gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu-Damboa da misalin karfe 2:20 na safiyar Talata
- Fashewar bam din ta rushe gadar gaba ɗaya, lamarin da ya katse hanyar da ke haɗa kauyen Mandafuma da garin Biu
- Wannan hari na ta’addanci na da nufin dakile zirga-zirgar mutane da motoci a hanyar, tare da haifar da matsala ga al’umma
- Hakan na kuma nufin hana ƙarfafa dakarun soja da ke ƙoƙarin shiga yankin don ɗaukar matakin tsaro daga Biu ko Damboa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Biu, Borno - Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne daga ISWAP sun yi ta'adi a kan hanyar Biu zuwa Damboa da ke jihar Borno.
Maharan sun ta da bam a gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu zuwa Damboa, da misalin karfe 2:20 na safiyar Talata 15 ga watan Afrilun 2025.

Asali: Original
Rahoton Zagazola Makama ya ce fashewar bam din ta lalata gadar gaba ɗaya, wanda hakan ya katse hanyar da ke haɗa kauyen Mandafuma da garin Biu cikin Jihar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram sun dasa bam a Borno
A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa an samu asarar rayuka a jihar Borno bayan wani bam da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa ya fashe a jihar Borno.
Fashewar bam ɗin ta auku ne a kan hanyar Damboa zuwa birnin Maiduguri a ranar Asabar, 12 ga watan Afirilun 2025.
Lamarin ya jawo asarar rayukan matafiya da bam ɗin ya tashi da su yayin da wasu da dama daga cikinsu suka samu raunuka.

Asali: Twitter
'Yan ta'adda sun tarwatsa gada a Borno
Wannan harin ta’addanci na da nufin hana zirga-zirgar jama’a da motoci a hanyar, tare da jefa su cikin matsin rayuwa da cikas.
Harin kuma na da manufa ta dakile shigowar ƙarin dakarun soja da ke bin hanyar domin taimaka wa wajen tabbatar da tsaro a yankin.
Martanin wasu daga cikin mutane kan harin
Masu ta'ammali da kafofin sadarwa sun yi martani kan harin da ya yi sanadin hana al'umma zirga-zirga a yankin Borno.
@keanaelmua:
"Idan har sun fara raba gadoji, to suna shirin karbe ikon ƙauyuka ne."
@im_jamib:
"Menene ke faruwa a kasar Najeriya haka."
@ibrahimYusifSa4:
"Duk ranar da ka bude 'data' abin takaici ne zai fara yi maka maraba."
'Yan Boko Haram sun farmaki sansanin sojoji
Mun ba ku labarin cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hare-hare a wasu sansanonin sojoji da ke jihar Borno lokacin da ake sa ran cin karfinsu.
Miyagun sun kai hare-haren ne a sansanonin sojojin da ke ƙananan hukumomin Damboa da Gambaru Ngala a ranar Litinin 24 ga watan Maris din shekarar 2025.
Motar sojojin wacce ke raka sabon kwamandan rundunar Operation Hadin Kai da aka tura Damboa ta taka nakiyar da ƴan ta’addan suka birne ne a kan titin Maiduguri-Damboa-Biu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng