Yadda Tinubu Ke Gyara Ɓarnar da Buhari Ya Yi na Karɓar Bashin $400bn saboda Naira
- Sanata Olamilekan Adeola ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta aro $400bn don daidaita darajar naira, lamarin da ya shafi tattalin arziki
- Ya jinjinawa gwamnatin Tinubu bisa cire tallafin mai da sauran sauye-sauye da ke nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya
- Adeola ya bayyana cewa Najeriya ta ci bashin tiriliyan don biyan tallafin man fetur da 'yan kasa da kashi daya ke cin gajiyarsa
- Sanatan ya yabawa Gwamna Dapo Abiodun bisa goyon bayansa, yana kuma alkawarin ci gaba da kawo ayyukan ci gaba ga al'ummar Ogun ta Yamma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Sanata Olamilekan Adeola ya caccaki salon mulkin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Sanata Adeola ya bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ta aro bashin $400bn domin daidaita darajar Naira da Dala.

Asali: Twitter
Tattalin arziki: An yabawa salon mulkin Bola Tinubu
Sanata Adeola ya bayyana hakan ne a taron ganawa da jama’a da aka gudanar a Ayetoro da ke jihar Ogun, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan majalisar, wanda ke wakiltar Ogun ta Yamma ya yabawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa ceton tattalin arzikin Najeriya.
Adeola, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa ya ce Tinubu ya ceto tattalin kasa ta hanyar cire tallafi.
Ya kara da cewa manufofi da sauye-sauyen Shugaba Tinubu sun kasance ne don amfanar ‘yan Najeriya da kuma wadanda za a haifa nan gaba.
Sanatan ya ce gwamnatin ta aro tiriliyan na Naira domin biyan tallafin man fetur, inda kasa da kashi daya na ‘yan Najeriya ke amfana.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su kara hakuri da gwamnatin yanzu, yana tabbatar da cewa manufofin tattalin arzikin suna fara haifar da sakamako mai kyau.

Asali: Facebook
Sanata ya tallafawa al'ummar yankinsa
Sanatan ya bayyana cewa an shirya bikin gudanar da tallafawa al’umma domin nuna godiya ga goyon bayan da suka bayar a zaben 2023.
Ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan ci gaba kamar na wutar lantarki, cibiyoyin sadarwa na zamani, asibitoci, kasuwanni, da gina hanyoyi a yankinsa.
Adeola ya bayyana cewa dalibai 3,000 daga kananan hukumomi shida za su samu tallafin karatu da kyautar N200,000 da kuma N100,000.
Ya kara da cewa shirin tallafawa da aka gudanar a Imeko-Afon ranar Juma’a, za a ci gaba da gudanar da shi a sauran yankuna.
Sanatan ya bukaci jama’a da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin da ke ci yanzu a jihar domin tabbatar da cigaban da ake so.
Buhari ya yi ta'aziyyar mutuwar Fafaroma Francis
Kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rasuwar Fafaroma Francis a matsayin babban rashi ga Kiristocin duniya.
Buhari ya kara da cewa duniya ba za ta manta da irin jagorancin da Fafaroma ya nuna ba, wanda ya haɗa da gaskiya, adalci da kula da talakawa.
Tsohon shugaban kasar ya jinjinawa Fafaroma Francis saboda yadda ya ba da muhimmanci ga rayuwar marasa galihu, masu bukata ta musamman da ‘yan gudun hijira.
Asali: Legit.ng