2027: Na Kusa da Buhari Ya Fadi Abin da Zai Tarwatsa Hadakar 'Yan Adawa

2027: Na Kusa da Buhari Ya Fadi Abin da Zai Tarwatsa Hadakar 'Yan Adawa

  • Faruk Adamu Aliyu ya yi magana kan shirin haɗakar ƴan adawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ke jagoranta
  • Na kusa da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa APC ba za ta bari ƴan adawa su ƙwace mulki a hannunta ba
  • Hakazalika 'dan siyasar ƴa musanta jita-jitar da ke cewa ƙusoshin tsohuwar jam'iyyar CPC na shirin ficewa daga APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Faruk Adamu Aliyu na kusa da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi magana kan batun ficewar ƙusoshin CPC daga jam'iyyar APC.

Faruk Aliyu ƙaryata jita-jitar cewa ƙusoshin na tsohuwar jam’iyyar CPC za su fice daga APC mai mulki.

Faruk Aliyu ya ce 'yan CPC ba za su fice daga APC ba
Faruk Aliyu ya musanta cewa kusoshin CPC za su fice daga APC Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Faruk Aliyu ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan CPC ba za su fice daga APC ba

Tsohon ɗan majalisar wakilan ya ce babu dalilin da zai sanya ɓangaren CPC da ke cikin APC ya fice daga jam’iyyar.

“Ba gaskiya ba ne, babu wani abu makamancin cewa mambobin tsohuwar CPC suna shirin ficewa daga APC."
"Takardarmu, wato takardar rajistar CPC, na daga cikin abubuwan da aka haɗa suka kafa APC. To, ta yaya za mu fice? Ina za mu tafi? Wannan ita ce jam’iyyarmu."

- Faruk Adamu Aliyu

Na kusa da Buhari ya taɓo batun haɗaka

Faruk Adamu Aliyu ya kuma taɓo batun haɗakar ƴan adawa wacce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar yake jagoranta.

Ya bayyyana cewa jam'iyyar APC ba za ta bari haɗakar ƴan adawan ta zo ta ƙwace mulki a hannunta ba.

Ya ƙara da cewa batun zaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa, shi ne abin da zai ruguza haɗakar ƴan adawan.

Tsohon mataimakin marasa rinjaye na majalisar wakilan ya kuma bayyana cewa Buhari bai amince da ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, daga APC zuwa jam’iyyar SDP ba.

Ya ce bai kamata El-Rufai ya rusa ginin da aka kafa da shi ba don kawai bai samu muƙamin minista ba.

Juga-jigan CPC
Jiga-jigan CPC sun ce ba za su fice daga APC ba Hoto: Tinubu Media Team
Asali: Twitter

An ba shugabannin jam'iyyar APC shawara

Hakazalika Faruk Adamu Aliyu ya buƙaci shugabannin APC da su haɗa kai da dukkan ɓangarori da ke cikin jam’iyyar domin rage takara da rigingimu kafin zaɓe mai zuwa.

"Siyasa tana buƙatar tattaunawa, siyasa tana buƙatar a kare muradun mutane da dama. Wannan shi ne abin da muke cewa, a ƙara tattaunawa da mutane, ba kawai daga tsohuwar CPC ba, har da daga PDP ma. Don haka a 2027, za a sami ƙananan rigingimu."

- Faruk Adamu Aliyu

Atiku ya magantu kan shirin haɗakar ƴan adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana shirin da ƴan adawa ke yi kan haɗaka.

Atiku ya bayyana cewa sun shirya rungumar kowane dandali domin ganin cewa sun raba Shugaba Bola Tinubu da mulki a zaɓen 2027.

Atiku ya bayyana cewa tafiyar ƙawancen ƴan adawan ta ɗauki saiti domin ganin cewa sun ƙwato mulki a hannun jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng