Mataimakin Gwamna da Ministan Tinubu Sun Yi Yunkurin ba Hammata Iska a gaban Shettima

Mataimakin Gwamna da Ministan Tinubu Sun Yi Yunkurin ba Hammata Iska a gaban Shettima

  • Wasu rahotanni sun nuna an samu hatsaniya tsakanin mataimakin gwamnan Bauchi, Auwal Jatau da ministan waje, Yusuf Tuggar
  • Hatsaniyar ta auku ne a cikin wata mota da ke ɗauke da mutanen biyu tare da mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima
  • Tun kafin faruwar lamarin, ana ganin cewa dangantaka tsakanin Amb. Tuggar da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ta baci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - An yi yunƙurin ba hammata iska tsakanin mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Jatau, da ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar.

Rikicin tsakanin manyan mutanen guda biyu ya jawo an dambace a tsakaninsu a ranar Juma'a.

An samu sabani tsakanin ministan Tinubu da mataimakin gwamnan Bauchi
Mataimakin gwamnan Bauchi ya yi fada da Yusuf Tuggar Hoto: Yusuf Tuggar, Ibrahim Sade
Asali: Facebook

An yi rikici tsakanin minista da mataimakin gwamna

Jaridar Leadership ta ce lamarin ya faru ne a cikin wata motar bas da ke ɗauke da su daga filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Abubakar Tafawa Balewa zuwa cikin birnin Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga wata muhawara mai zafi da ta fara tsakanin Gwamna Bala Mohammed da ministan waje.

Sai dai lokacin da mataimakin gwamnan, Auwal Jatau, ya shiga cikin batun domin kare gwamnan, rigimar ta ƙara ƙamari, wanda hakan ya tilasta sauran fasinjojin cikin motar su shiga tsakani don hana rikicin ya kai inda ba a so.

Ba a ga maciji tsakanin minista da gwamnan Bauchi

Idan za a iya tunawa dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Bala Mohammed da ministan harkokin wajen.

Dangantakar ta yi tsami ne bayan tsauraran kalaman da gwamnan ya yi kan manufofin Shugaba Bola Tinubu, musamman ƙudirin gyaran haraji, wanda ya ce zai ƙara jefa yankin Arewa cikin talauci.

Yusuf Tuggar ya mayar da martani yana kare dokar gyaran haraji, yana mai cewa an tsara ta ne da adalci ba tare da nuna wariya ga wani yanki na ƙasar ba.

Haka kuma, a watan Maris na wannan shekarar, Yusuf Tuggar ya ƙi halartar wani taron kaddamar da shirin "Irrigate Nigeria" a ƙauyensu Udubu, wanda gwamnatin tarayya ta shirya.

Ana zargin ya ƙauracewa taron ne domin gujewa haɗuwa da Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne babban baƙo a wajen taron. Yusuf Tuggar ne ya kamata ya wakilci Shugaba Tinubu a wurin taron.

Wasu sun ce an yi mari sakamakon rikicin

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa wai Auwal Jatau ya kai wa ministan mari a lokacin rikicin.

An kuma rahoto cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ministan lafiya Farfesa Ali Pate, da wasu sanatoci suna cikin motar da lamarin ya faru.

Mataimakin gwamnan Bauchi, Auwal Jatau
An yi hatsaniya tsakanin Auwal Jatau da Yusuf Tuggar Hoto: Ibrahim Sade
Asali: Facebook

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun gwamnan jihar Bauchi, Mukhtar Gidado, ya ƙi yin tsokaci kan jita-jitar.

Ya ce bai shaida faruwar lamarin ba, kuma babu wanda ya ba shi cikakken bayani a kai.

Wani da ke kusa da Tuggar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda ba shi da hurumin magana a kai, ya tabbatar da cewa rikici ya faru tsakanin mataimakin gwamnan da ministan.

Ya kuma ƙara da cewa mataimakin gwamnan ya shiga cikin lamarin domin goyon bayan ubangidansa. Sai dai bai tabbatar da cewa an yi dambe tsakaninsa da ministan ba.

Matawalle ya caccaki masu sukar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya caccaki ƴan siyasar Arewa masu sukar Shugaba Bola Tinubu.

Matawalle ya bayyana cewa ƴan siyasan da ke sukar Tinubu suna yin hakan ne kawai domin su yi suna a siyasance.

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce yawancin masu sukar suna yin hakan ne domin sun kasa samun muƙamai a gwamnatin Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng