Sojoji Sun Kama Dan Bindiga 'Dogo' bayan an Dade Ana Farautar Shi a Daji

Sojoji Sun Kama Dan Bindiga 'Dogo' bayan an Dade Ana Farautar Shi a Daji

  • Dakarun Rundunar Sojin Najeriya ta 6 da Operation Whirl Stroke sun cafke ɗan bindiga da ake nema ruwa a jallo da kuma wani sojan karya
  • An gudanar da samamen ne a yankuna daban-daban na Taraba a ƙarƙashin aikin Operation Lafiyan Jama’a da ke yaki da miyagun laifuffuka
  • Sojojin sun kuma gano makamai da harsasai da kayan sojoji a samame daban-daban da suka kai daga ranar 16 zuwa 24 ga Afrilu, 2024

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba- Sojojin Najeriya sun kama wasu manyan masu laifi da ake nema tare da gano makamai da kayan soja a wasu samame da aka kai cikin makonni biyu a jihar Taraba.

An gudanar da wadannan ayyukan tsaron ne a ƙarƙashin Operation Lafiyan Jama’a da ke yaki da ‘yan bindiga da masu tada hankalin jama’a a yankunan jihar.

Dan Bindiga
Sojoji sun kama Dogo da wani sojan bogi a Taraba. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

A sakon da Zagazola Makama ya wallafa a X, sojojin sun kai samamen ne tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar leƙen asiri ta DIA a kananan hukumomin Lau, Donga, Bali da Gassol.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama dan bindiga, Dogo a Taraba

A ranar 16 ga Afrilu, sojojin sun samu kiran gaggawa daga wani mafarauci a yankin Dutsen Kachalla da ke Lainde, karamar hukumar Lau kan wasu 'yan bindiga.

Yayin da suka kai farmaki wurin, ‘yan bindigar sun tsere amma sojojin sun gano rigar soja da katin zama dan kasa mai dauke da sunan Adamu Umaru Jauro.

A ranar 19 ga Afrilu, sojojin sun kama wani mai suna Yusuf Hammadu da aka fi sani da “Dogo” a Lainde Jessy.

An bayyana cewa yana cikin jerin masu laifi da aka dade ana nema saboda garkuwa da mutane da karɓar kuɗin fansa a Jalingo, Ardo-Kola, Lau da Yorro.

An kama sojan karya a jihar Taraba

A wani samame daban da aka kai ranar 22 ga Afrilu, an kama Richard Ongu da ke karyar cewa soja ne, inda ya bayyana cewa tsohon jami’in sojan sama ne da aka sallama tun 2019.

Ongu yana damfarar mutane da sunan soja, ya yaudari dillalin mota ya karɓi mota mai darajar Naira miliyan 5.2 da kuma N1.6m.

Baya ga haka, an ruwaito cewa Richard Ongu yana karɓar kuɗi daga iyaye da sunan zai saka ‘ya’yansu a soja.

Sojoji sun gano makamai a yankin Donga

Ranar 24 ga Afrilu, sojojin tare da jami’an DIA sun kai samame yankin Jatau-Nyimu da ke Donga, suka gano harsasai 86, bindigogi uku, kayan sojoji da rediyo kirar Beofeng.

Kwamandan Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yabawa sojojin bisa ƙwazon da suka nuna.

Sojoji
An yaba wa sojoji bisa kama dan bindiga da ake nema ido rufe. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Kwamandan Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yabawa sojojin bisa ƙwazon da suka nuna.

An kama mutane 3 da bindiga a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun 'yan sanda sun kama wasu mutane uku dauke da bindiga a jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin mutanen da hannu a kashe kashe da ake a jihar duk da ana cigaba da bincike.

An kama mutanen ne yayin da matsalar tsaro ta kara ta'azzara a jihar inda aka kai munanan hare hare da suka salwanta rayuka da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng