An ba Sojoji Wa'adin Murkushe 'Yan Ta'addan Mahmuda da Suka Bulla a Arewa

An ba Sojoji Wa'adin Murkushe 'Yan Ta'addan Mahmuda da Suka Bulla a Arewa

  • Babban hafsan rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya umarci dakarun soji da su kawar da sabuwar ƙungiyar ta’addanci a yankunan Kwara
  • Oluyede ya ce Najeriya ba za ta iya amincewa da sake yaduwar ƴan ta’adda zuwa wasu sassa ba, yana mai ƙarfafa gwiwar dakarun a barikin Soji da ke Ilorin
  • Janar Oluyede ya bayyana cewa gwamnati za ta bayar da duk wata gudummawa da ake buƙata domin dakile 'yan ta'addan da suka bulla a Arewa ta Tsakiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Shugaban sojojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayar da umarni ga dakarun soji da su gama da sabuwar ƙungiyar 'yan ta’adda a jihar Kwara.

Ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara barikin sojoji na Sobi da ke Ilorin, inda ya gana da dakarun da za a tura domin kawar da barazanar ƙungiyar Mahmuda a jihar.

Olufemi Oluyede
Olufemi Oluyede ya ba sojoji umarnin murkushe kungiyar Mahmuda. Hoto: HQ Nigeria Army
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da shugaban sojin ya yi ne a cikin wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laftanar Janar Oluyede ya ce ya zama wajibi a shawo kan ƙalubalen da wuri, domin hana ƙungiyar yaduwa zuwa sassan Najeriya kamar yadda aka taɓa fuskanta da Boko Haram.

Bukatar kawar da Mahmuda a wata 1

Shugaban hafsan sojin ya bayyana cewa ba ya son ganin kowane ɗan ta’adda a yankin da ke kewaye da Kainji Dam bayan wata ɗaya.

Laftanar Janar Oluyede ya ce:

“Ba zan so in ga burbudin waɗannan miyagun mutanen a cikin daji ba bayan wata ɗaya. Ku tabbatar kun fatattake su gaba ɗaya.”
“Idan suna son komawa wata ƙasa daban, ba matsala, amma dole ku tabbatar kun kore su daga wannan yanki gaba ɗaya,”
Sojoji
Laftana Janar Oluyede na ganawa da sojoji a Kwara. Hoto: HQ Nigeria Army
Asali: Facebook

Oluyede: 'Ba za a bar 'yan Mahmuda su yadu ba'

Laftanal Janar Oluyede ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta lamunci bullar wata sabuwar ƙungiya kamar Boko Haram a ƙasar ba.

A karkashin haka ya bayyana cewa sojojin za su samu dukkan goyon baya da kayan aikin da ake buƙata domin cimma nasara a yaki da 'yan ta'addan.

A wata hira da ya yi da manema labarai, Oluyede ya bayyana cewa matsalar ba ta da yawan gaske, kuma za a magance ta kai-tsaye cikin lokaci ƙanƙani.

Rahoton Channels TV ya nuna cewa Laftanal Janar Oluyede ya ce:

“Ina tabbatar muku, cikin wata ɗaya za ku ga canji. Abin da ke faruwa a Kwara ba zai zama barazana ga zaman lafiyan Najeriya gaba ɗaya ba,”

An kashe 'Dan daba, Baba Beru a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wani kasurgumin dan daba da ake kira Baba Beru ya hadu da ajalin shi bayan arangama da 'yan sanda.

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sanda sun kama Baba Beru za su tafi da shi sai abokan shi suka fara kai hari wa jami'an tsaron.

A lokacin da ake arangama tsakanin 'yan sanda da 'yan daban aka harbi Baba Beru, kuma likitoci sun tabbatar da mutuwar shi a asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng