Tinubu Ya Gana da Fubara a Karon Farko, ana Hasashen Dawo da Gwamna Ofis
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da aka dakatar a birnin London
- Wannan shi ne haduwar su ta farko tun bayan ayyana dokar ta-baci a Rivers, kuma an ce sun tattauna ne kan rikicin jihar
- Ana sa ran Tinubu zai gana da Fubara, Nyesom Wike da 'yan majalisar jihar domin samun daidaito kan rikicin siyasar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
London - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da aka dakatar, a wata ganawa ta musamman da ta gudana a birnin London.
Ganawar ta biyo bayan dogon rikicin siyasa ne da ya dabaibaye jihar wanda ya kai ga sanya dokar ta-baci.

Asali: Facebook
Jaridar the Africa Report ta tabbatar da cewa Fubara ne ya nemi ganawar, inda suka tattauna batutuwa da dama da suka shafi makomar siyasar jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ita ce ganawa ta farko tun bayan da Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers ranar 18 ga Maris, ya kuma sauke Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, daga mukamansu.
Me Tinubu da Fubara suka tattauna?
Punch ta wallafa cewa rahotanni daga fadar shugaban kasa sun nuna cewa ganawar ta fi karkata ne wajen nemo mafita ga halin da jihar Rivers ke ciki.
Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Tinubu ya jaddada cewa rikicin siyasar jihar ya zama barazana ga zaman lafiyar kasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi, inda ya ce rikicin ya hana gudanar da gwamnati yadda ya kamata.
Ya nada tsohon hafsun rundunar sojan ruwa, Ibok-Ete Ekwe Ibas, a matsayin shugaba mai rikon kwarya a jihar.
Sai dai gwamnoni daga jihohin PDP sun kai kara kotun koli domin kalubalantar wannan mataki na shugaban kasa, suna neman dawo da doka da tsarin mulki.
Rade radin mayar da Simi Fubara ofis
Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba, wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce ana duba yiwuwar dawo da Fubara ofis kafin wa’adin wata shida ya cika.
Majiyoyin sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, kuma yanzu ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, bai halarci ganawar ba.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Nyesom Wike bai ji daɗin ganawar da aka yi tsakanin Tinubu da Fubara ba tare da saninsa ba.

Asali: Facebook
Ana sa ran Tinubu zai gudanar da wata ganawa nan gaba da Fubara, Wike da 'yan majalisar dokokin jihar domin samar da mafita da za ta dawo da zaman lafiya a jihar Rivers.
Tinubu ya yi kira ga Musulman Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola ya yi kira ga Musulman Najeriya da su rungumi nuna tausayi da adalci.
Bola Tinubu ya yi jawabin ne a wani taron wata kungiyar Musulmi da aka yi a jihar Ogun a makon da ya wuce.
Legit ta rahoto cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya samu wakilcin mataimakiyar gwamnan jihar Ogun ne yayin taron kasancewar a lokacin yana hutu a Faransa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng