Tinubu Ya Yi Kira ga Musulman Najeriya ana tsaka da Caccakar Shi
- Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga musulmai da su kasance jakadun zaman lafiya, adalci da tausayi a halin da duniya ke ciki
- Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin bude taron kasa na Ansar-ud-Deen karo na 11 da aka gudanar a Abeokuta, Jihar Ogun
- Tinubu ya yaba da rawar da Ansar-ud-Deen ke takawa wajen yada ilimi da ci gaban tun kusan shekaru 100 da suka wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Musulman Najeriya da su ci gaba da zama jakadun gaskiya, zaman lafiya da tausayi.
Mai girma Shugaban kasar ya ce akwai bukatar hakan a irin wannan lokacin da ake ƙara nuna bambancin addini da al’adu a duniya.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana haka ne yayin bude taron kasa na Ansar-ud-Deen karo na 11 wanda aka gudanar a Abeokuta, Jihar Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasar, wanda mataimakiyar gwamnan Ogun, Noimot Salako-Oyedele ta wakilta, ya bayyana cewa taron ya zo daidai da halin da ake ciki.
Kiran da Tinubu ya yi wa Musulmai
Bola Tinubu ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin Musulmi da sauran al’ummar da suke rayuwa tare da su.
The Nation ta wallafa cewa Tinubu ya ce:
“A duniyar da ke ƙara cika da bambancin ra’ayi da al’ada, dole ne Musulmi su kasance masu adalci, tausayi da son zaman lafiya.
Shugaban ƙasar ya yabawa ƙungiyar Ansar-ud-Deen bisa gudummawar da take bayarwa a fannin ilimi da ci gaban ƙasa.
Bola Tinubu ya ce ƙungiyar Ansar-ud-Deen ta zama ginshiƙi mai ƙarfi a cikin tsarin zamantakewar Najeriya.
Tinubu ya ce gwamnatinsa na tafiya daidai
Tinubu ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta jajirce wajen daura Najeriya a kan turba mai kyau.
Shugaban ya kara da cewa shirinsa na Renewed Hope ya mayar da hankali kan farfaɗo da tattalin arziki da tallafa wa talakawa.
Ya buƙaci wakilan taron da su yi amfani da damarsu wajen yin nazari mai zurfi, fitar da sababbin dabaru da kuma bayar da shawarwari masu amfani don karfafa addinin Musulunci.
Bayanin shugaban Jamb a wajen taron
Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya shawarci 'yan Ansar-ud-Deen da su kasance masu hakuri da juna, yada alheri, nuna ƙauna da zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al’umma.
Shugaban ƙungiyar Ansar-ud-Deen na kasa, Alhaji Abdulrafiu Sanni, ya ce tun kafuwar ƙungiyar a shekarar 1923, ta kasance a sahun gaba wajen inganta ilimi da ci gaban al’umma.

Asali: Facebook
Tinubu zai dawo Najeriya daga Faransa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai dauko hanya daga Faransa zuwa Najeriya a yau Litinin.
Legit ta rahoto cewa fadar shugaban kasa ce ta sanar da haka bayan an matsa ma shi lamba kan zaman da yake yi a Faransa.
Tun bayan tafiyar Bola Tinubu Faransa ake cigaba da kashe kashe da suka jawo kiran shi ya bar abin da yake ya dawo gida Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng