Sabuwar Kungiyar Ƴan Ta'adda Ta Bayyana a Arewacin Najeriya? Gaskiya Ta Fito

Sabuwar Kungiyar Ƴan Ta'adda Ta Bayyana a Arewacin Najeriya? Gaskiya Ta Fito

  • Rahoton da ake yaɗawa cewa sabuwar ƙungiyar ta'addanci ta ɓulla a jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya ba gaskiya ba ne
  • Jami'an tsaro sun bayyana cewa Mahmouda da ake ta surutu da zargin kungiya ce, wani kwamandan Boko Haram ne da ya yi ƙaurin suna
  • Legit Hausa ta tattaro cewa a kwanakin baya ƴan sanda sun musanta zargin da ake yi cewa yan ta'adda sun fara shiaiga jihar Kwara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - A ƴan kwanakin nan, an fara yaɗa rahoton cewa sabuwar kungiyar ta'addanci ta bayyana a jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Wannan labari ya ɗaga hankulan jama'a musamman mazauna Kwara da Arewa baki ɗaya duba da taɓarɓarewar tsaron da ake funkanta tsawon shekaru a yankin.

Jihar Kwara.
Jami'an tsaro sun musanta bullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Jihar Kwara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A rahoton da Daily Trust ta wallafa, ta ce al'umma sun fara fargaba bayan bullar sabuwar kungiyar mai suna Mahmouda a wasu sassan jihar Kwara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa kungiyar ta fara tayar da hankali a yankunan da ke makwabtaka da filin shakatawa na Kainji.

Menene gaskiyar wannan rahoto?

Legit Hausa ta gano cewa wannan rahoto ba gaskiya ba ne kuma Mahmouda da ake fargaba ba sabuwar ƙungiya ba ce, wani kwamandan kungiyar Boko Haram ne.

Jami'an tsaron Najeriya ne suka karyata rahoton, inda suka bayyana cewa babu wani abin fargaba domin babu wata sabuwar kungiyar ta'addanci da aka kafa a Kwara.

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Ya ce sahihan bayanai sun nuna cewa babu wata sabuwar kungiya da aka kafa; mutumin da ake kira Mahmouda ba sabuwar kungiyar ta’addanci ba ce, sanannen kwamandan Boko Haram ne.

Wanene Mahmuda, kwamandan Boko Haram?

Mahmouda dai ya shafe lokaci yana fafatawa da dakarun hukumomin tsaro a Jihar Borno kafin ya koma jihar Kaduna, inda ya hadu da ƙasurgumin ‘dan ta’adda, Sadiku.

Daga bisani, ya tashi zuwa yankin Shiroro da Rafi a jihar Neja, ya ƙulla alaka da ragowar kungiyar Darul Salam, yana daukar matasa da tilasta musu bin doka ta tsattsauran ra’ayi, musamman Fulani makiyaya.

Yanzu kuwa, rahotannin sirri sun tabbatar cewa Mahmouda da wasu daga cikin mayakansa sun matsa zuwa cikin dazukan da ke kan iyaka da jihar Kwara.

A rahoton da Zagazola Makama ya wallafa ya ce ɗan ta'addan ya fara hada kai da wasu ‘yan bindiga da suka dade suna kai hare-hare a yankin Arewa maso Yamma.

Wannan dai ba sabon rukuni bane, sai dai reshen Boko Haram da ke aiki tare da ‘yan bindiga a sababbin wurare.

Dakarun soji.
Mahmouda da kungiyar ta'addanci ba ce in ji jami'an tsaro Hoto: Nigerian Army
Asali: UGC

Barazanar da ake fuskanta

Wannan karin bayani na zuwa ne bayan hukumar ‘yan sanda ta musanta rahotannin kwanakin baya da suka yi ikirarin cewa ƴan ta'adda na kwarara zuwa Kwara.

Yanzu da abubuwan suka fara bayyana, jama’a na tambayar shin me jami’an tsaro za su ce yanzu? Don a ganinsu wannan ba ƙaramar barazana ba ce.

Masana tsaro na gargadin cewa idan ba a dakile wannan barazana ba, Kwara na iya zama sabon cibiyar rikici kamar yadda ya faru da wasu jihohi a baya.

Sun buƙaci a ƙara inganta harkokin tattara bayanan sirri da tura dakarun musamman da kuma kafa sansanoni a dazukan da ke tsakanin Neja da Kwara domin murkushe wannan hadari tun kafin ya kazanta.

Ƴan ISWAP sun rusa gadar sama a Yobe

A wani labarin, kun ji cewa ƴan ta'adda da ake zargin mayaƙan kungiyar ISWAP ne sun rusa gada a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas.

Rahonni sun nuna cewa ƴan ta'addan sun yi amfani da bam wajen tarwatsa gadar da ke haɗa Ngurbuwa da Goniri a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan harin ya jefa mutanen yankin cikin halin kunci musamman wajen tsallaka rusasshiyar gadar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262