Mahmuda: Sabuwar Kungiyar Ta'addanci a Arewa Ta Zafafa Hare Hare
- Sabuwar ƙungiyar ta’addanci da ake kira Mahmuda ta ƙara kaimi wajen kai hare-hare a ƙananan hukumomin Baruten da Kaiama a jihar Kwara
- Aƙalla mutane shida, ciki har da matashi dan shekara 19 da wani ɗan sa-kai, sun rasa rayukansu a harin da aka kai Ilesha Baruba da Kemaanji
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyara Kaiama tare da jami’ai domin duba matsalar da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara - Tashin hankali ya sake barkewa a wasu sassan jihar Kwara da ke iyaka da jihar Niger sakamakon hare-hare da wasu gungun ‘yan bindiga da ake kira Mahmuda suka kai.
Harin ya zo ne makonni bayan rahotanni sun bayyana yadda ‘yan ta’addan ke ta kashe-kashe da sace-sacen jama’a a yankunan da ke kusa da dajin Kainji.

Asali: Twitter
Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun dira kasuwar dare da ke Kemaanji a Baruten da misalin karfe 9:30, suka fara bude wuta kan jama’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa an kashe mutane shida ciki har da Fulani hudu, ɗan sa-kai guda, da wani matashi da harsashi ya same shi yayin da yake wucewa.
Hare haren da Mahmuda ke kai wa
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa harin na iya zama na ramuwar gayya sakamakon zargin hadin gwiwa da jami’an tsaro da wasu mutanen yankin ke yi.
Harin da aka kai a Kaiama a ranar da lamarin ya faru ya kuma hallaka wani ɗan sa-kai a wani yanki, wanda hakan ke nuna cewa hare-haren an tsara su ne da gangan.
Ƙungiyar Mahmuda na cigaba da kai hare-hare da sace mutane a kauyuka da dama kamar Kemaanji, Tenebo, Nanu, da Baabete a jihar Kwara da kuma Babana da Wawa a jihar Niger.
Gwamna AbdulRazaq ya kai ziyara Kaiama
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyara Kaiama tare da manyan hafsoshin tsaro domin tattaunawa da masarauta da sauran shugabanni.
A cewarsa, harin da aka kai ramuwar gayya ce da ‘yan ta’adda ke yi wa ‘yan sa-kai saboda hadin gwiwar su da jami’an tsaro.
Trust TV ta wallafa cewa gwamnan ya ce:
“Muna aiki tare da sojoji, sun kai ziyara wurin, sun tattauna da jama’a, kuma muna da tabbacin za mu dawo da zaman lafiya.”
Farooq Kperogi ya wallafa a X cewa 'yan kungiyar Mahmuda sun kai hare hare kan al'ummar Kaiama bayan ziyarar gwamnan domin nuna fushinsu.
Fitaccen Farfesan da ya ke karantarwa a Amurka ya fito ne daga yankin Baruten a jihar Kwara wanda ke iyaka da kasar Benin.
Yadda Mahmuda ta samo asali
Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar Mahmuda ta fito daga Mokwa a jihar Niger kuma sun karɓe dajin Kainji shekaru fiye da biyar da suka wuce, suka kori masu gadin dajin.
Wasu rahotanni na cewa ƙungiyar Mahmuda reshe ce da ta balle daga Boko Haram ƙarƙashin Shekau.
Sai dai a wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta musanta wanzuwar ƙungiyar Mahmuda da kuma kashe ‘yan sa-kai da ake zargin sun yi.

Asali: Facebook
Bulama Bukarti ya ce 'yan ta'adda na kara karfi
A wani rahoton, kun ji cewa lauya mai sharhi kan lamuran tsaro, Audu Bulama Bukarti ya ce 'yan ta'adda na kara karfi a Najeriya.
Bulama ya ce a yanzu haka Boko Haram tana rike da wasu yankunan jihar Borno ta inda ko 'yan siyasa ba su iya ziyartar mazabunsu.
Ya kara da cewa 'yan ta'adda na karbar miliyoyin kudin fansa a yankunan Arewa ta Yamma da sauran wurare domin samun kudin sayen makamai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng