Tsohon Shugaban Majalisa Ya Roƙawa Tinubu Alfarmar Talakawa
- Tsohon shugaban majalisa Ahmad Lawan da Etsun Lokoja, Emmanuel Akamisoko Dauda-Shelika sun bukaci addu’a ga Shugaba Bola Tinubu
- Haka kuma sun roki jama'a da su rika yi wa sauran shugabannin Najeriya addu’a don samun nasarar kawar da matsalolin Najeriya
- A bangarensa, Sanata Ahmad Lawan na ganin lokacin bikin Easter da Kiristocin kasar nan ke yi, dama ce ta sabunta hidima ga kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Etsu Lokoja, Emmanuel Akamisoko Dauda-Shelika, sun bukaci ‘yan Najeriya da su rika yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a.
Sun bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda suka ce yin addu’a ga shugabannin kasar, musamman shugaban kasa, na da matukar muhimmanci wajen samar da hadin kai da ci gaba a Najeriya.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Sanata Ahmad Lawan ya bayyana hakan cikin sakon sa na bikin Easter, inda ya bukaci ‘yan kasa da su kawar da bambance-bambance da ke barazana ga hadin kan kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A yiwa Tinubu, kasa addu’a,” Tsohon Shugaban Majalisa
Dr. Ahmad Lawan ya bayyana cewa akwai matukar bukatar a rika yiwa shugabannin Najeriya addu’a domin samun nasarar shawo kan kalubalen da kasa ke fuskanta.
Ya ce:
“Yayin da ‘yan’uwanmu Kiristoci ke bikin Easter — lokaci ne na sabuntawa da fatan alheri — mu duba mu tuna da dabi’un da suka hada mu a matsayin kasa daya."
“Kamar yadda Almasihu ya shawo kan kalubale, haka ma Najeriya ta za ta shawo kan matsalolinta."
Tsohon shugaban majalisar ya nemi hadin kai
Sanatan ya bukaci ‘yan Najeriya da su sabunta niyyar su na gina kasa mai dunkulalliya, wacce kowa zai yi alfahari da ita.

Asali: Facebook
Ya kara da cewa:
“Mu bari wannan lokaci na Easter ya zame mana dama na zama ‘yan kasa nagari, masu tausayi, da masu bayar da gudummawa ga ci gaban kasa.
“Mu dage wajen ganin mun tsaya tsayin daka wajen adalci, gaskiya da daidaito ga kowa da kowa a Najeriya.
“Mu yi amfani da wannan lokaci wajen tabbatar da gaskiya a cikin Najeriya da kuma aiki tukuru domin samun makoma cike da zaman lafiya da arziki.”
Ya nanata cewa bai kamata jama'a su manta da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wajen addu'o'in samun nasara da iya mulki ba.
Tinubu zai dauki mataki a kan tsaro
A baya, kun samu labarin cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya daga tafiyar aikin da ya kai kasashen Turai na tsawon makonni biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa ya shirya taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro da ministocin tsaron kasar domin tattauna matsalolin rashin kwanciyar hankali da ke kara ta’azzara.
Majiyoyi sun ce tun bayan tafiyar Tinubu, an samu rahotanni da dama masu tayar da hankali, ciki har da kashe fiye da mutane 120 a hare-hare da dama da suka auku a jihohi uku a kasar nan.
Asali: Legit.ng