Jira Ya Kare: Yanzu Tinubu Ya Fara Hada Kayansa, Zai Hau Jirgi Ya Dawo Najeriya

Jira Ya Kare: Yanzu Tinubu Ya Fara Hada Kayansa, Zai Hau Jirgi Ya Dawo Najeriya

Abuja - Fadar shugaban kasar Najeriya ta kawo karshen guna-gunin da ake yi game da rashin dawowar Shugaba Bola Tinubu gida daga Faransa.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar Litinin, 21 ga watan Afrilu, fadar shugaban kasar ta bayyana takamaimai ranar da Shugaba Tinubu zai dawo gida, bayan hutunsa a Paris.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, cewa Shugaba Bola Tinubu zai hau jirgi ya dawo gida yau Litinin.

Sanarwar da Onanuga ya fitar na cewa:

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida yau."

'Yau' da Onanuga ya furta, na nufin ranar Litinin, 21 ga Afrilu, wadda ta yi daidai da ranar Easter, bikin Kiristoci na gicciyen Yesu Almasihu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.