Osun 2026: Kananan Hukumomi 8 da Ka Iya Tasiri Wurin Samar da Mai Nasara a Zaɓen

Osun 2026: Kananan Hukumomi 8 da Ka Iya Tasiri Wurin Samar da Mai Nasara a Zaɓen

  • Zaben gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta ya fi karkata kan Adeleke, Oyebamiji da Salaam, wadanda duk suka fito daga Osun ta Yamma
  • Osogbo, Olorunda, Ife Central, Ife ta Gabas, Ife ta Kudu, Odo Otin, Iwo da Ilesa ta Gabas na cikin manyan kananan hukumomin jihar
  • Adeleke na dogaro da ayyukan raya kasa da karfin Ede, yayin da Oyebamiji da Salaam ke neman samun gagarumar nasara a wasu muhimman kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - A yau Asabar 15 ga watan Agustan 2026 ake gudanar da zaben gwamnan Osun takarar tsakanin gwamna mai ci Ademola Adeleke, Bola Oyebamiji da Najeem Salaam ta kara tsauri

Dukkan manyan ‘yan takarar uku sun fito daga mazabar Osun ta Yamma, lamarin da ya sa rabon kuri’u ke iya zama mai matukar zafi.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da za su iya sa gwamna Adeleke doke APC a zaben Osun

An fara zaben gwamnan Osun a yau Asabar
Najeem Salam na ADC, Gwamna Ademola Adeleke na Accord da Bola Oyebamiji na APC Hoto: Najeem Salam, Ademola Adeleke, Bola Oyebamiji.
Source: Twitter

Yankin da Adeleke da Salaam suka fito

Adeleke da Salaam sun fito daga mazabar tarayya ta Ede ta Arewa, Ede ta Kudu, Egbedore da Ejigbo, yayin da Oyebamiji ya fito daga Irewole, Isokan da Ayedaade, cewar Punch.

Adeleke na dogaro da ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekaru hudu domin samun kuri’un jama’a musamman daga Ede da makwabtanta

Mataimakinsa Kola Adewusi da tsohon sakataren PDP na kasa, Farfesa Wale Oladipo, na kokarin kara masa kuri’u a Ife Central, Ife ta Gabas da Ife ta Kudu

Tsohon SSG na Osun, Moshood Adeoti, wanda ya fito daga Iwo, shi ma yana kokarin taimakawa Adeleke wajen samun nasara a mazabar Iwo.

Tasirin da Ademola a zaben Osun
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da ake zaben gwamna. Hoto: Ademola Adeleke.
Source: Instagram

Osun: Abin da ka iya rage tasirin Adeleke

Sai dai kasancewar mataimakin Oyebamiji, Benjamin Adereti, dan Ile-Ife ne na iya rage karfin Adeleke a kananan hukumomin Ife uku

Dan takarar APC na Sanata, Amos Ogunbiyi, na iya zama cikas ga Adeleke a Iwo, yayin da goyon bayan Iyiola Omisore zai iya taimaka wa Oyebamiji.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Abubuwa 5 da za su iya taimakon APC ta karbe jihar Osun

Oyebamiji na sa ran samun kuri’u masu yawa a mazabarsa, inda tsohon dan takarar gwamna, Dotun Babayemi, ke kokarin taimaka masa a yankin Gbongan.

Goyon bayan bangaren PDP karkashin tsohon gwamna Olagunsoye Oyinlola na iya kara karfin Oyebamiji a Odo Otin, yayin da ake sa ran ya yi karfi a Boluwaduro.

Oyebamiji ana ganin zai yi karfi a Boripe, Irepodun, Ife ta Arewa da Obokun, yankunan da ke da alaka da tsohon gwamna Adegboyega Oyetola.

Ana ci gaba da shirye-shiryen zaben gwamna a Osun
Taswirar jihar Osun da ake gudanar da zaben gwamna. Hoto: Legit.
Source: Original

Tasirin da Saalam zai iya yi a zaɓen

Najeem Salaam, tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Osun na tsawon shekaru takwas, na ci gaba da kasancewa dan takara mai karfin gaske a zaben.

Baya ga Ejigbo, inda yake da karfi, ana sa ran Salaam zai yi kyau a Ilesa ta Gabas, Osogbo da Olorunda saboda tasirin tsohon gwamna Rauf Aregbesola.

Sai dai alakar Salaam da Aregbesola na iya zama kalubale, musamman wajen samun karin karbuwa a wasu sassan Osun.

Osun: Kananan hukumomi da ka iya yin tasiri

Ban da manyan ƙananan hukumomin yan takarar gwamna a zaɓen, ana ganin waɗannan ƙananan hukumomi za su taka rawa wajen yanke wanda zai yi nasara.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: 'Yan takarar gwamna 2 sun janye, sun mara wa Adeleke baya

Wasu daga cikin ƙananan hukumomin da ake ganin suna da tasiri sun haɗa da:

Osogbo

Olorunda

Ife ta Tsakiya

Ife ta Gabas

Ife ta Kudu

Odo Otin

Iwo

Ilesa ta Gabas

Gwamna Adeleke ya zargi tsohon gwamna Oyetola da amfani da karfin gwamnatin tarayya wajen kawo cikas ga yakin neman zabensa.

A wani muhawarar Arise TV, Adeleke ya ce an kama wasu ‘yan Accord, yayin da daya daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar ke tsare a Abuja

Ya ce ya tuntubi Bishop Matthew Kukah domin shiga tsakani kafin ya amince da halartar taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Dabarar da APC ke yi kan zaben Osun

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa APC za ta lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa APC za ta lashe zaben ne ta hanyar tsarin siyasarta, ba tare da dogaro da tasirin gwamnatin tarayya ba.

Hakan na zuwa ne yayin ake fafatawa a zaben gwamnan Osun a yau Asabar 15 ga watan Agustan shekarar 2027 wanda ake ganin za ta yi matukar zafi musamman tsakanin Accord, APC da kuma ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.