Karo na biyu, TY Danjuma Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Dau Bindigu Su Kare Kansu

Karo na biyu, TY Danjuma Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Dau Bindigu Su Kare Kansu

  • Janar TY Danjuma ya sake caccaki jami'an sojoji inda ya zargesu da kashi a wando kan rikicin yan bindiga
  • Tsoho Sojan ya jadadda kira ga yan Najeriya su taimaki kansu su nemi bindiga don kare kansu
  • Bayan shekara daya na nada shi, an baiwa sabon Sarkin Wukari a jihar Taraba sandar mulki

Taraba - Tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya) a ranar Asabar ya jaddada kira ga yan Najeriya su tashi tsaye su kare kansu daga hare-haren yan bindiga da suka addabi kasar.

TY ya bayyana hakan ne a taron mikawa sabon Aku Uka na garin Wukari, Manu Ali, sandar mulki a garin Wukari, jihar Taraba, rahoton NAN.

Gwamna Darius Ishaku na Taraba ya nada sabon sarkin ne tun 2021 sakamakon mutuwar Sarki Shekarau Angyu da ya kwashe shekaru 45 kan karagar mulkin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Danuma
Karo na biyu, TY Danjuma Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Dau Bindigu Su Kare Kansu Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

TY Danjuma ya ce kiran da yayi da yan Najeriya shekarun baya na cewa su kare kawunansu daga yan ta'adda amma akayi watsi da maganarsa gashi an gani yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Rokon da nike maka sabon Aku Uka shine ka hada kawunanmu domin kare kansu daga makiya kasar nan."
"A 2017 da nayi kira ga mutane su kare kansu, wata kwamitin karya da aka kafa tayi bincike kan lamarin tace karya nike saboda babu hujja."
"Yau a kasar nan, ga hujja kowa na gani; yan bindiga daga kasashen ketare na kashe mutane suna kwace musu filaye."
"Ba zan baku makamai ba, ku je ku gano yadda yan bindiga ke samun nasu kuma sai ku samo."

Daga cikin wadanda suka halarci taron mika sandar mulkin akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad III, Gwamna Simon Laloong na Plateau dss.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Zan Gina Sabuwar Jami'ar Kiristoci A Jihar Neja, TY Danjuma

A makon da ya gabata, Janar Theophilus Danjuma, ya bayyana cewa zai gina sabuwar jami'ar Cocin Anglican na farko a Arewacin Najeriya.

Danjuma yace zai yi wannan gini ne a garin Dikko, jihar Neja kuma za'a sanyawa wannan jami'a suna Walter Miller.

A jawabin da ya gabatar ranar Laraba a Legas yayin liyafar dare, TY Danjuma ya bayyana cewa shekaru biyu da suka gabata suka fara shawaran gina jami'ar bayan ganawarsa da wasu Bishap-Bishap.

Yace tuni an kaddamar da shiri sosai wajen fara ginin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel