Yadda 'Yan Sa Kai Suka Hallaka Matashi saboda Mace a Neja
- Wani matashi ya rasa ransa a jihar Neja a hannun jami'an tsaro na ƴan sa-kai bayan sun lakaɗa masa dukan kawo wuka
- Mambobin na ƙungiyar ƴan sa-kai sun hallaka matashin ne bayan wata rigima ta haɗa su saboda wata mace
- Jami'an tsaro na ƴan sanda sun fara gudanar da bincike domin tabbatar da cewa wanda aka kashen ya samu adalci
- Ƴan sa-kan waɗanda suka aikata ɗanyen aikin sun tsere yayin da jami'an ƴan sanda suka fara farautarsu da niyyar cafke su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Ana zargin wasu ƴan ƙungiyar sa-kai da hallaka wani matashi a jihar Neja.
Ana dai zargin ƴan sa-kan ne da kisan Muhammad Omaba sakamakon wata rigima da ake yi a kan mace.

Asali: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan sa-kai suka kashe matashi a Neja
Majiyoyi sun bayyana cewa a ranar Alhamis, 17 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, an karɓi ƙorafi dangane da mutuwar Muhammad Omaba, wanda yake zaune a ƙauyen Cuderegi da ke cikin ƙaramar hukumar Lemu Gbako ta jihar Neja.
Waɗanda ake zargi da kisan su ne, Alhaji Yikangi, Modu Alhaji Idris, Danjuma Yikangi, Worongi Yikangi, da kuma wani da ake kira Mai Tawhidi.
Dukkanin waɗannan mutane an bayyana su a matsayin mambobin wata ƙungiyar tsaro ta sa-kai da ke aiki a cikin ƙauyen.
Majiyoyin sun bayyana cewa ƴan sa-kan sun kai wa marigayin hari da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar da lamarin ya faru.
An bayyana cewa hatsaniyar ta samo asali ne daga wata muhawara da ta ɓarke tsakaninsu dangane da wata mata mai suna Fatima Suleiman, wadda ita ma ƴar ƙauyen Cuderegi ce.
Wannan rigima ta rikiɗe zuwa fada, inda aka dinga dukan Omaba har sai da ya suma.
Bayan dukan da aka yi masa, an garzaya da shi zuwa wanu asibiti a Lemu domin samun agajin gaggawa, amma likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan an kai shi.
Ƴan sanda sun fara gudanar da bincike

Asali: Twitter
Hukumar ƴan sanda ta tabbatar da cewa tana ci gaba da gudanar da bincike, tare da ƙaddamar da farautar waɗanda ake zargin domin a kama su a gurfanar da su a gaban shari’a.
A halin yanzu, waɗanda ake zargin sun tsere, amma jami’an tsaro na ƙoƙarin ganin an kamo su domin su fuskanci hukunci kan wannan mummunan aiki da suka aikata.
Ƴan sanda sun cafke ƴan sa-kai a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na ƴan sanda sun yi caraf da wasu mambobin ƙungiyar sa-kai a jihar Neja.
Ƴan sandan sun cafke ƴan sa-kai guda uku bisa zargin kashe wani matashi a ƙaramar hukumar Rijau ta jihar.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa ƴan sa-kan sun harbe matashin ne lokacin da yaje shingen bincikensu yana kan babur.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng