Shekarau Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Shugabannin da Za Su Ceto Najeriya

Shekarau Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Shugabannin da Za Su Ceto Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ys shawarci ƴan Najeriya kan su zaɓi shugabanni nagari
  • Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar shugabanni nagari domin ceto ta daga ƙalubalen da take fuskanta
  • Tsohon sanatan ya nuna cewa ya kamata ƴan Najeriya su zaɓi shugabanni nagari ba tare da la'akari da jam'iyyar da suka fito ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana irin shugabannin da ake buƙata domin ceto Najeriya.

Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa shugabanni masu gaskiya da riƙon amana ne kaɗai za su iya ceto Najeriya daga halin da take ciki.

Ibrahim Shekarau
Shekarau ya ba 'yan Najeriya shawara Hoto: Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a jiya a lokacin taron ƙasa karo na 27, wanda cibiyar addinin Musulunci ta ƙasa ta shirya a sansanin Alhazai na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya haɗa manyan malamai na addini, jami’an gwamnati, shugabannin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Wace shawara Shekarau ya ba da?

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa, duk da ƙalubalen da ake fuskanta a halin yanzu.

Shekarau ya buƙaci Musulmi da su zaɓi shugabanni masu cikakkiyar cancanta da ƙima, a kowace jam’iyya suke ciki, matuƙar sun nuna halin gaskiya da amana a aikinsu.

Shekarau ya jaddada cewa matsalolin da ke addabar al’ummar Musulmi za a iya shawo kansu idan aka samu haɗin kai da jajircewa.

"Ina bada shawarar cewa mutane su zaɓi shugabanni nagari, ko da kuwa daga jam’iyyar shaiɗan suke."

- Sanata Ibrahim Shekarau

Shekarau
Shekarau ya ba 'yan Najeriya shawara Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Yadda aka kafa ƙungiyar Muslim Umma

A jawabinsa na maraba da mahalarta taron, Shugaban ƙungiyar Muslim Umma na ƙasa, Farfesa Muhammad Babangida Muhammad, ya bayyana cewa cibiyar addinin Musulunci ta ƙasa an kafa ta ne a shekarar 1980.

Ya ce daga mambobin ƙungiyar ɗalibai Musulmi, waɗanda suka yi niyya su ci gaba da yi wa al’ummarsu hidima bayan sun kammala karatu ne suka kafa ta.

Ya bayyana irin nasarorin da ƙungiyar ta samu cikin shekaru sama da 50, musamman wajen ƙarfafa haɗin kai, ingantaccen shugabanci, da haɗin kan al’umma.

Yayin da yake nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, Farfesa Babangida ya buƙaci dukkan matakan gwamnati da su ba noma da koyon sana’o’i fifiko domin daƙile rawar da matasa ke takawa a cikin ayyukan ta’addanci da aikata laifuka.

Shekarau ya yi magana kan haɗaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan haɗakar jam'iyyun ƴan adawa.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa babu wata haɗakar ƴan adawa da za ta iya kawar da jam'iyyar APC a babban zaɓen shekarar 2027.

Shekarau ya bayyana cewa haɗakar ɗa ƴan adawan suke shiryawa ba su da wakilcin shugabannin jam'iyyunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng