Ban yi danasanin bautawa Najeriya a karkashin Jonathan ba – Sambo
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, yace bai yi nadama ba a lokacinda yayi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Sambo ya bayyana hakan a wani jawabi da yayi a ranan Lahadi, 23 ga watan Satumba yayinda ya kai ziyarar jaje a Toru-Orua, mahaifar gwamnan jihar Baylsa, Seriake Dickson, wanda yayi rashin mahaifiyarsa kwanakin baya.
Sambo ya bayyana cewa dole yayi wa Allah godiya saboda dama da ya bashi na yiwa kasar hidima a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Asali: Depositphotos
Tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda yabayyana cewa a halin yanzu Bankin Afrexim da African Union ta nada shi a matsayin jakada don gudanar da aikin baja koli tsakanin kasashen Afurka a Cairo, babban Birnin Egypt yayi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da tayi abunda ya dace a zaben 2019 da za a gudanar.
KU KARANTA KUMA: Kwastam sun kashe wani mai shigo da shinkafa ta barauniyar hanya a Katsina
Sambo yace, “banyi nadama ba a lokacin da na yiwa Najeriya hidima. Na gode wa Allah da ya bani daman yiwa Kasarmu hidima.
“Daga farko dai, nazo ne don mika jaje ga dan uwana da yar uwata kan rashi na mahaifiyarsu da suka yi kuma muna rokon Allah ya kara wa iyalan hakurin jurewa rashin."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng