Kwanaki da Barin NNPCL, an Taso Mele Kyari a Gaba kan Zargin Badakalar $1.5bn
- Wata kungiya ta kwararru da 'yan ƙasa masu kishin Najeriya ta bukaci a binciki tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari, kan kashe $1.5bn
- Kungiyar ta yabawa Bola Tinubu bisa sauke Kyari, tare da cewa an zuba makudan kudi a gyaran matatar mai ba tare da haifar da 'da mai ido ba
- Kungiyar ta ce akwai buƙatar kwakkwaran bincike kan bacewar ganga miliyan 89 na danyen mai da kuma yarjejeniyar mai da kamfanin Matrix
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wata kungiya ta hadin gwiwa ta kungiyoyin fararen hula sun bukaci a binciki tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Dr Mele Kyari.
Kungiyoyin sun bukaci bincikensa ne kan yadda aka kashe $1.5bn a matatar mai ta Port Harcourt.

Asali: Facebook
An yabawa Tinubu kan cire Mele Kyari
Da yake jawabi yayin taron manema labarai a Abuja, jagoran kungiyar, Michael Omoba, ya yaba da matakin Bola Tinubu na sauke Kyari daga mukaminsa, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya zama dole du jawo hankalin shugabanni na cikin gida da na waje kan zargin babbar sata da aka yi a NNPCL karkashin Mele Kyari.
Ya ce:
“Dukkanmu mu na da kishin ƙasa, shi ya sa dole mu fadi gaskiya a bayyane, musamman game da wannan babban rikici na amanar jama’a.
“Muna da yakinin cewa domin ba sabbin shugabannin NNPCL dama su yi aiki da gaskiya, wajibi ne a binciki kudaden da aka kashe a cikin shekaru 5.
“Yanzu dai babu shakka cewa sauke Kyari ya yi daidai kuma ya zo da wuri, ganin yadda NNPCL ta koma tamkar ƙungiyar sirri mara bincike.
“Abin da ya fi ta da hankali shi ne yadda aka zub da $1.5bn kan matatun Port Harcourt biyu, amma babu wani sakamako a fili."

Asali: Facebook
NNPCL: An bukaci binciken Mele Kyari
Omoba ya ce abin takaici ne yadda aka zuba makudan kudi a matatar da bata aiki madadin inganta kasa, cewar TheCable.
Ya ce ya kamata a binciki wannan barna da aka yi da dukiyar jama'a domin tabbatar da adalci wa yan kasa.
Ya kara da cewa:
“Lallai irin wannan barna da aka yi da kudin jama’a ya kamata ta jawo bincike da kama duk masu hannu, ciki har da ƙasashen waje.
“Shugaban ƙasa Tinubu yana ba da dama ga ‘yan Najeriya su fadi gaskiya. Mutane na tambaya, ina kudin? Me ya faru da matatun?
“Abin takaici ne yadda aka zubar da wadannan kudade ba tare da wani abin nunawa ba, lamarin da ya fallasa salon mulkin Kyari.
'Dalilin' cire Kyari da Tinubu ya yi
Kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi garambawul a kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) kwanakin baya.
Tinubu ya sauke Mele Kyari da mambobin kwamitin gudanarwa na NNPCL sannan ya maye gurbinsu da wasu sababbi.
Jami'ai a fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa wannan sauyin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na bunƙasa ɓangaren mai a Najeriya.
Asali: Legit.ng