Gaskiyar Abin da Ya Faru da Jonathan a Lokacin Jinyar Yar’adua Inji Sanata Yar’adua

Gaskiyar Abin da Ya Faru da Jonathan a Lokacin Jinyar Yar’adua Inji Sanata Yar’adua

  • Abdulaziz Musa Yar’adua ya shaidawa Najeriya abubuwan da suka faru a bayan fage da jinyar tsohon shugaban kasa
  • ‘Danuwan na Ummaru Musa Yar’adua ya musanya zargin cewa shugaban kasar bai rubuta takardar sallama shugabanci ba
  • Sanata Abdulaziz Yar’adua ya ce a lokacin da suke asibiti, sun fahimci an yi nufin mika mulki ga Dr. Goodluck Jonathan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kusan a karon farko, Abdulaziz Musa Yar’adua ya fito ya yi magana game da halin da Najeriya ta tsinci kanta a 2009-2010.

An samu gibin shugabanci sakamakon rashin lafiyar shugaba Ummaru Musa Yar’adua, aka ci karo da tangarda a mika mulki

Yaradua
Marigayi Ummaru Musa Yar'adua da Sanata Abdulaziz Yaradua Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abdulaziz Yar'adua ya wanke Sanata Yar'adua

Kara karanta wannan

Attajiri ya bukaci 'yan Najeriya su marawa Tinubu baya, ya fadi lokacin samun sauyi

Kanin tsohon shugaban na Najeriya ya shaidawa tashar Channels yadda ya damu da ya ji ana cewa ‘danuwansa bai mika mulki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua ya ce yana cikin wadanda suke rika jinyar Marigayi tsoshugaba Yar’adua a Saudi Arabiya.

Ummaru Yar'adua ya hana Goodluck Jonathan mulki?

Abdulaziz Yar’adua ya tabbatar da kafin shugaba Yar’adua ya bar Najeriya, ya rubuta takardar mika iko ga Dr. Goodluck Jonathan.

Tsohon sojan ya dauko labarin yadda Goodluck Jonathan bayan zama shugaban rikon kwarya ya tura tawaga ta ga mai gidansa.

Bayan wannan yunkuri ne Sanatan na Katsina ta tsakiya ya ce suka shirya dawo da shugaban kasar Najeriya yana halin ciwon ajali.

Yar'adua ba zai cigaba da mulki ba

A lokacin ne Marigayi Yar’adua ya fadawa Abdulaziz da likitansa cewa babu yadda zai iya cigaba da mulki a irin yanayin da yake ciki.

Kara karanta wannan

"Yadda aka sace takardar da Marigayi Yar'adua ya rubuta lokacin jinya a Saudiyya"

‘Dan majalisar ya kawo wannan ne domin ya nuna ‘danuwansa bai dage sai ya rike shugabanci alhali bai da isassashiyar lafiya ba.

Yayin da yake gadon ajali ya ji ana kokarin maido shi Aso Rock, Yar’adua ya ce ko mahaukaci ya san ba zai iya zuwa ofis a haka ba.

Matsayar dangin marigayin shi ne Yar’adua ya rubuta wasika domin Dr. Goodluck Jonathan ya zama shugaban rikon kwarya.

Abdulaiz Yar’adua wanda yana gidan soja abubuwan suka faru, ya yi kira ga ‘yan jarida suka rika bincike sosai kafin wallafa labari.

El-Rufai ya bi layin El-Rufai

Kuna da labari cewa Hon. Muhammad Bello El-Rufai ya yi bayanin gudumuwar da Malam Nasir El-Rufai ya ba shi a lokacin kamfe.

Duniya ta ji yadda aka gamsar da tsohon Gwamnan Kaduna a kan yaransa ya fito takarar ‘dan majalisa, a yau yana karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel