'Dan Sandan Najeriya Ya Sha Giya Ya Bugu, Ya Harbe Wani Mutumi Har Lahira
- An shiga fargaba da wani jami’in ‘yan sanda ya kashe mutum ɗaya a yankin Maitumbi da ke jihar Neja, bayan ya sha giya da ya bugu
- Majiyoyi sun ce jami’in da ake zargi yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Maitumbi, ya shiga harbin ba ji ba gani bayan buguwarsa
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja ya ba da umarnin fara bincike kan lamarin, yayin da ake neman jami'in da ya yi kisan ruwa a jallo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - A ranar Litinin ne al'ummar Maitumbi da ke jihar Neja suka shiga cikin tashin hankali yayin da wani jami'in rundunar 'yan sandan Najeriya ya kashe wani mutumi.
An rahoto cewa, jami'in dan sandan, da ba a bayyana sunansa ba, ya samu wasu mutane ya bude masu wuta bayan ya kwankwadi giya, ya bugu.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yaran Bello Turji sun sace ɗan Isiyaka Rabiu, matashin ya yi roko a bidiyo

Asali: Twitter
Makakken dan sanda ya yi kisan kai a Neja
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa yanzu haka rundunar 'yan sandan jihar Neja ta fara neman jami'in ruwa a jallo yayin da ta soma bincike kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Shuwala Danmamman, ya umarci shugaban ofishin 'yan sanda na Maitumbi (DPO) da ya kamo jami'in da ya yi wannan aika-aika.
Majiyoyi sun shaida cewa jami'in da ake zargi da wannan aika-aika yana aiki ne a ofishin 'yan sanda na Maitumbi, kuma ya kwankwadi barasa mai yawa kafin aikata laifin.
An ce bayan ya sha giyar da ta fi karfin kwakwalwarsa, ya dauki bindigarsa, sannan ya fara harbin jama'ar da ke kusa da shi, ba ji ba gani.
"Ya kashe Sani a ya na barci" - Majiya
A yayin harbin, ya kashe wani mutum da aka bayyana sunansa da Sani kawai a unguwar Angwan-Kaje da ke karamar hukumar Chanchaga.

Kara karanta wannan
Ramadan: Direba ya murkushe sufetan ɗan sanda da ke bakin aiki a masallacin Abuja
Shaidu sun bayyana cewa jami’in ya kuma yi kokarin harbin wani mai sayar da shayi da ake kira Mai Shayi, amma ya samu damar tserewa da ransa.
Wata majiya ta ce:
“Jami’in ya harbi Sani a lokacin da yake barci. Bayan haka, ya yi yunkurin harbin Mai Shayi, amma ya tsere. An tarar da harsashin bindiga a wurin."
Rundunar 'yan sanda za ta hukunta jami'inta

Asali: Twitter
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ga manema labarai a ranar Talata, inji Sahara Reporters.
Wasiu Abiodun ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike, kuma za a hukunta jami’in da ya aikata kisan bayan kammala binciken.
“Rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton harbin da aka yi a unguwar Angwan-Kaje, Maitumbi, Minna, da misalin karfe 3:00 na daren ranar 10 ga watan Maris, 2025.
“Kwamishinan ‘yan sanda ya umurci DPO na Maitumbi da ya gano jami’in da ya aikata laifin domin daukar matakin da ya dace a kansa.
“Za a sanar da jama’a ci gaban binciken da kuma matakan da aka dauka nan gaba'"
- Inji Wasiu Abiodun.
'Dan sanda ya saki masu laifi a cikin maye
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani jami'in 'yan sanda da ya sha giya ya bugu a Zambia ya saki masu laifi 13 daga ofishin hukumar domin su yi murnar sabuwar shekara.
Jami'in mai suna Sifeta Titus Phiri ya saki masu laifin ya na cikin halin maye, yana mai cewa suma suna da 'yancin yin shagalin sabuwar shekara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng