Akwai Matsala: Sarki Sanusi II da Aminu Ado Sun Canza Shawara kan Hawan Sallah a Kano
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da Sarki na 15, Aminu Ado Bayero sun hakura da yin hawan Sallah a lokacin bukukuwan babbar Sallah
- Sarakunan biyu sun bayyana cewa sun dakatar da hawa ne saboda dalilai na tsaro da kuma shawarwarin rundunar 'yan sandan Najeriya
- Tun farko dai an ruwaito cewa hawan zuwa masallacin idi da sarakunan biyu suka yi a ranar Sallah ya jefa jama'a cikin fargaba da damuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Sarakuna biyu da ke ikirarin kujerar sarautar Kano, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun sanar da dakatar da dukkanin hawan Sallah da suka shirya.
An bayyana matakin ne a taruka daban-daban da aka gudanar, inda aka ce an dauki wannan mataki ne bisa matsalolin tsaro da kuma umarnin jami’an tsaro.

Source: Twitter
Daily Trust ta tattaro cewa tun da farko dai, Sanusi da Bayero sun sanar da shirinsu na gudanar da bukukuwan hawan Sallah daban-daban a lokacin babbar Sallah.
Sanusi II ya fadi dalilin soke hawan Sallah
Da yake magana a madadin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, Matawallen Kano, Alhaji Aliyu Ibrahim, ya ce sun soke hawan Sallah.
Ya ce majalisar masarautar ta samu rahotannin tsaro da ke nuna cewa wasu mutane na shirin amfani da bukukuwan hawan Sallah domin tada hankalin jama’a da haddasa rikici a Kano.
Ya bayyana cewa an dauki matakin dakatar da hawan ne domin kauce wa tabarbarewar zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaro a jihar yayin bukukuwan babbae Sallah.
Aminu Ado Bayero ya bi sahun Sanusi II
Hakazalika, Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, ya sanar da dakatar da hawan Sallah a madadin Sarkin Kano na 14, Aminu Ado Bayero.
Ya ce an dauki matakin ne domin bin umarnin rundunar ‘yan sanda da nufin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.
Dan’agundi ya ce su masu biyayya ne ga doka kuma za su mutunta umarnin jami’an tsaro domin kare zaman lafiya a jihar.

Source: Facebook
A ranar Laraba, sarakunan biyu sun yi hawan Sallah wanda Sarki da jama'arsa ke hawa dawaki zuwa filin idi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Sai dai hakan ya sa mutanen Kano suka fara nuna damuwa kan shirin sarakunan biyu na gudanar da sauran bukukuwan hawan Sallah, wanda a al'ada ake yi a wuri iri daya.
A halin yanzu dai Sanusi II da Aminu Ado sun hakura da yin hawan Sallah bisa dalilan tsaro da kuma shawarwarin rundunar yan sanda.
Sanusi II ya ja hankali kan fasahar AI
An ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce Najeriya na cikin bukatar gaggawa wajen tsara manufofi kan fasahar zamani musamman AI.
Khalifa Muhammadu Sanusi ya ce ana bukatar tsarin musamman don dadaita yadda ake amfani da fasahar AI, wajen bunkasa ci gaban kasa mai dorewa.
Ya bukaci jami’o’in Najeriya su jagoranci samar da taswirar AI ta kasa, yana mai jaddada cewa dole ne su sauya tsarin koyarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


