Mayakan ISWAP Sun Kai Hari Borno, Sun Yi Barna kafin Isowar Sojoji
- 'Yan ta'adda dauke da miyagun makamai sun kai farmaki kan sansanin Fulani da ke zaune a karamar hukumar Damboa ta Jihar Borno
- Harin ya jefa jama'a cikin firgici, ganin yadda 'yan ta'addan suka bude wuta kan bayin Allah ba su ji ba su gani ba a yankin Tolmari
- An tabbatar da cewa wani magidanci da dansa sun samu munanan raunuka, yayin da mayakan suka tsere zuwa cikin dajin da ke kusa
- Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu rahoto kan harin, sannan sun yi kokarin kai dauki cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno — Ana zargin cewa wasu mayakan kungiyar 'yan ta'addan ISWAP sun kai hari kan wani sansanin Fulani makiyaya a jihar Borno.
Harin ya faru ne a kusa da garin Tolmari da ke cikin karamar hukumar Damboa, inda aka raunata wasu mazauna yankin.

Asali: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan ISWAP sun afkawa sansanin makiyayan a safiyar Alhamis da misalin 2:00 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ‘yan ISWAP suka farmaki Borno
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun shigo ne a kafa, sannan suka bude wuta kan mazauna yankin ba tare da nuna bambanci ba.
Wani daga cikin majiyoyin ya ce:
“Wani mai suna Ali Mai, mai shekaru 50 da haihuwa daga garin Tolmari, ya ji mummunan rauni a kansa, yayin da aka harbi dansa mai shekaru 28, Ali Mai Abba a kafa.”
Harin ISWAP: Sojoji sun kai agaji a makare
Bayan samun rahoton harin, sojojin Najeriya a karkarshin atisayaen hadin kai sun gaggauta isa wurin domin kai dauki. Sai dai kafin su iso, ‘yan ta’addan sun tsere zuwa cikin daji.

Kara karanta wannan
Sojoji da ‘yan ta’adda sun gwabza bayan harin ofishin ‘yan sanda, an samu asarar rayuka

Asali: Twitter
An garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa Asibitin karamar hukumar Damboa domin samun kulawar likitoci.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji sun kara kaimi a yaki da ‘yan ta’addan a yankin, domin dakile hare-haren da suke kaiwa a cikin yankunan jihar Borno.
Sojoji sun gwabza da 'yan ISWAP
Harin da mayakan ISWAP su ka kai Damboa na zuwa ne bayan sojojin Najeriya sun dakile wani hari da suka kai ofishin 'yan sanda da ke Malari.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin sun yi wa mayakan ISWAP jina jina a lokacin da suka yi yunkurin sace wadansu motocin yakin jami'an tsaron.
An kashe mayakan ISWAP a Borno
A baya, mun wallafa cewa wani mummunan fada ya barke tsakanin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP, wanda ya haddasa mutuwar daruruwan mayakan da ke addabar jama'a a Borno da kewaye.
Wannan al'amari ya afku ne a lokacin da mayakan Boko Haram, karkashin jagorancin Bakoura, suka kai farmaki kan sansanonin ISWAP a karamar hukumar Abadam.
Da farko 'yan kungiyar ISWAP sun yi kokarin tsayawa don kare farmakin, amma mayakan Boko Haram sun fi karfinsu, suka hallaka shugabanninsu da dama, musamman daga kabilar Buduma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng