Hukumar RRS sun kai mace mai nakuda asibiti (Hotuna)

Hukumar RRS sun kai mace mai nakuda asibiti (Hotuna)

- RRS hukuma ce mai bada agajin gaggawa a Jihar Legas

- Mai cikin ta fara nakuda cikin motar haya har kan jinjirin ya fara fitowa

- An ki karban ta a asibiti mai zaman kan sa saboda bata da katin asibiti

Hukumar bada agaji na gaggawa, wanda a turance ake kira Rapid Response Squad, RRS, reshen Jihar Legas ta kai wata mata mai ciki zuwa asibiti a yayin da nakuda ya kamata a cikin motar haya.

Matar 'yar shekaru 30 da dan doriya tana cikin motar haya mai zuwa tsibirin Legas a yayin da nakuda ya kama ta sai ta fara kukan neman agaji alhali kan jinjirin ya fara fitowa.

Hukumar RRS sun kai mace mai nakuda asibiti
Hukumar RRS sun kai mace mai nakuda asibiti

Nan take jami'an hukumar RRS da ke kusa suka amsa kukan ta suka saka ta cikin motar su zuwa wani asibiti mai zaman kan sa amma aka ki karban ta a asibitin saboda bata da katin asibiti.

Hukumar RRS sun kai mace mai nakuda asibiti
Hukumar RRS sun kai mace mai nakuda asibiti

DUBA WANNAN: Zan ziyarci Nnamdi Kanu kwanan nan, Inji Sarkin Iwo, Abdurrashid Akanbi

Nan da nan Matar ta bada shawaran a kai ta asibitin haihuwa na tsibirin Legas wanda ba tare da bata lokaci ba suka karbe ta suka kaita dakin haihuwa.

Jami'an hukumar RRS din dai sun bar matar a hannun wasu mutum 3 da ma'aikatan asibitin kafin su koma kan bakin aikin su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164