Sojoji Sun Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga, an Samu Asarar Rayuka

Sojoji Sun Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga, an Samu Asarar Rayuka

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan bindiga a wani artabu da suka yi a jihar Zamfara a cikin kwanakin nan
  • Sojojin sun hallaka ƴan bindiga masu yawa bayan sun farmake su a sansaninsu da ke kasan wani tsauni a yankin Kaura Namoda
  • Bayanai sun ce jami'an tsaron sun yi raga-raga da ƴan bindigan bayan sun kai musu hari babu ƙaƙƙautawa ta sama da ƙasa
  • Daga cikin ƴan bindigan da aka kashe har da wani tantiri mai suna Babangida wanda yake riƙe da babban matsayi a cikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yanma sun ƙara matsa ƙaimi a ayyukan fatattakar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun kawar da wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Babangida tare da wasu miyagu da dama.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka shugaban dabar 'yan bindiga a Zamfara

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Zamfara
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka ragargaji ƴan bindiga

Majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da farmakin ne a ranar 10 ga watan Maris, 2025. Farmakin ya samu goyon bayan ɓangaren sojojin sama na Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin sun ƙaddamar da samame tun da sassafe a Dan Sa’adi, wani sansanin ƴan bindiga, wanda ke a ƙasan wani tsauni.

Wannan ya haddasa gagarumar musayar wuta tsakanin sojojin da ƴan bindigan, amma sojojin sun yi nasarar fatattakarsu bayan an kai hare-hare ta sama da ƙasa.

Wasu daga cikin ƴan bindigan da suka tsira sun tsere zuwa saman tsaunin, inda ɓangaren sojojin sama suka ci gaba da ragargazar su da hare-hare.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe ƴan bindiga da dama, ciki har da Babangida, wanda aka sani yana riƙe da babban matsayi mai muhimmanci a cikin su.

Kara karanta wannan

"An samu ci gaba": Matakin da mutane suka dauka don kawo karshen harin 'yan bindiga

An lalata makamai da dama tare da rushe sansanonin ƴan bindiga a yankin.

Sojoji sun lalata maɓoyar ƴan bindiga

A wani samamen na daban, sojojin sun yi raga-raga da wata maɓoyar ƴan bindiga a Gidan Rugga, ciki har da gidan wani da ake zargi da taimakawa ƴan bindiga.

Abubuwan da aka samu daga gidan sun haɗa da, kayan sojoji da baƙin takalmin sojoji guda ɗaya.

Bugu da ƙari, an gano wani shago da ake sayar da cajin rediyon Baofeng ga ƴan bindiga, inda aka banka masa wuta domin hana su amfani da hanyoyin sadarwa.

Haka nan, sojojin sun tsaftace tare da tabbatar da tsaro a hanyar Kungurki-Walo, wanda hakan zai inganta rayuwar mazauna yankin.

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram masu kai hare-hare a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun kai dauki bayan 'yan bindiga sun farmaki mutane, sun samu nasara

Dakarun sojojin sun hallaka wani kwamandan Boko Haram mai suna Abba Alai (Amirul Khahid na Alafa), wanda shi ne babban mai haɗa bama-bamai na ƙungiyar.

Sojojin sun hallaka kwamandan na Boko Haram ne a harin da suka kai a sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Gwoza.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng