Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga 40 bayan Sun Kawo Harin Ramuwar Gayya

Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga 40 bayan Sun Kawo Harin Ramuwar Gayya

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro, sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Zamfara
  • Sojojin sun yi nasarar daƙile wani harin ramuwar gayya da ƴan bindigan suka kawo bayan an kashe wani babba a cikinsu
  • Jami'an tsaron tare da haɗin gwiwar Askawaran Zamfara sun hallaka aƙalla ƴan bindiga 40 a artabun da suka yi a garin Mada

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma tare da haɗin gwiwar Askarawan Zamfara, sun ragargaji ƴan bindiga.

Dakarun sojojin sun samu nasarar daƙile wani harin ramuwar gayya da ƴan bindiga suka kawo a Mada, cikin ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Zamfara
Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Zamfara Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada.da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga a Zamfara

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka aƙalla ƴan bindiga 40 a yayin artabun da suka yi.

Harin da ƴan bindigan suka kawo ya biyo bayan kashe sani shugaban dabar ƴan bindiga, mai suna Alhaji Sani Dan Garin Bawo, da dakarun sojoji suka yi a wani farmaki.

Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan ƙarƙashin jagorancin Dogo Hamza, sun kawo harin ne kan ɗaruruwan babura.

Ƴan bindigan sun tattaru ne a ƙauyen Manya wanda yake wajen garin Mada kafin su kawo harin a ranar Talata, 11 ga watan Maris.

Bayan samun rahoton shirin kai harin, sojoji sun garzaya zuwa wajen garin Mada, suka fafata da ƴan bindigan tare da tallafin ƴan sa-kai.

Sai dai yayin da musayar wuta ta ƙara tsanani, wasu daga cikin ƴan bindigan sun kutsa cikin garin Mada, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.

Sojoji sun yi raga-raga da ƴan bindiga

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka shugaban dabar 'yan bindiga a Zamfara

Bayan aukuwar hakan, an turo ƙarin dakaru cikin gaggawa, lamarin da ya sa aka hana ƴan ta’addan cinna wuta ga gidaje, yin fashi ko sace mazauna garin.

Wani ganau ya bayyana cewa faɗan ya ɗauki awanni da dama, amma daga ƙarshe, jami’an tsaro da ƴan sa-kai sun yi nasarar fatattakar ƴan bindigan.

“Mun ƙirga kusan ƴan bindiga 40 da aka kashe, amma abin takaici, fararen hula huɗu sun rasa ransu."

- Wani ganau

Bayan fafatawar, sojoji sun ƙara ƙarfafa yawansu a Mada, domin hana sake aukuwar wata barazana ta tsaro.

Ana ɗaukar kashe Sani Dan Garin Bawo a matsayin gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga, duba da irin rawar da ya taka wajen shirya hare-hare, garkuwa da mutane da satar shanu a yankin.

Jami'an sojoji sun fatttaki ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar ragargazar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

"An samu ci gaba": Matakin da mutane suka dauka don kawo karshen harin 'yan bindiga

Sojojin sun ragargaji ƴan ta'addan ne bayan sun kai musu farmaki a maɓoyarsu da ke ƙasan wani tsauni.

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan bindiga masu yawa ciki har da wani babban hatsabibi wanda ya daɗe yana ayyukan ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng