Akpabio: Sanatan Arewa Ya Goyi Bayan Natasha kan Zargin Cin Zarafi? An Fede Gaskiya
- Ahmad Lawal ya yi magana kan rahotannin da ke cewa yana goyon bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zargin da take yi kan Godswill Akpabio
- Tsohon shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa ko kaɗan bai ɗauki wani ɓangare ba a cikin batun zargin cin zarafin da ake yi kan Akpabio
- Sanatan mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa ya bayyana rahotannin a matsayin tsantsagwaron ƙarya sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi watsi da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi magana kan zargin ya goyi bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zargin da take yi wa Godswill Akpabio.
Sanata Ahmad Lawan ya musanta rahotannin da ke cewa ya goyi bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Ɗan Majalisar da ya jagoranci dakatar da Sanata Natasha ya shiga matsala

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dr. Ezrel Tabiowo, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmad Lawan ya musanta goyon Natasha
Sanata Ahmad Lawan ya bayyana waɗannan rahotannin a matsayin tsantsagwaron ƙarya da rashin gaskiya.
Ya bayyana cewa maganganun da ya yi yayin zaman majalisar dattawa a ranar 6 ga watan Maris, 2025, ya yi su ne a bisa ƙa'ida.
Ya bayyana cewa maganganunsa sun kasance ne kawai kan batun tsarin aiki kuma ba su da wata alaƙa da zarge-zargen da ake yi wa Sanata Godswill Akpabio.
Dr. Ahmad Lawan, wanda ya kasance shugaban majalisar dattawa ta tara, ya bayyana cewa abin da kawai ya yi shi ne jan hankalin majalisar ka da ta amince da shawarwarin da kwamitin ladabtarwa ya bayar.
Kwamitin dai ya ba da shawarar janye jami’an tsaron Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
A cewarsa, amincewa da irin wannan matakin na janye jami'an tsaron, na iya zama barazana da za a iya amfani da ita a nan gaba wajen tauye ƴancin ƴan majalisar.
Shawarar da Sanata Ahmad Lawan ya gabatar domin yin gyara kan shawarwarin kwamitin, ba a amince da ita ba.
Sanata Lawan bai goyon bayan kowane ɓangare
“Babu wani lokaci da Sanata Ahmad Lawan ya goyi bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ko kuma ya ɗauki ɓangare a cikin zargin da ya shafi shugaban majalisar dattawa."
"Shiga tsakanin da ya yi ya ta’allaka ne bisa ƙa’ida, wanda hakan ya yi nuni da jajircewarsa wajen kare bin doka da oda."
- Ezrel Tabiowo
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya roƙi al’umma da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da duk da yake yaɗawa a kansa kan batun taƙaddamar Sanata Natasha da Akpabio.
Akpabio ya caccaki ƴan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya caccaki ƴan Najeriya masu muhawara kan dambarwar da ke faruwa a majalisa.
Godswill Akpabio ya bayyana cewa da yawa daga cikinsu suna muhawarar ne ba tare da sanin abin da suke magana a kai ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng