Akpabio: Majalisa Ta Lissafo Manyan Zunuban da Suka Sanya aka Dakatar da Natasha

Akpabio: Majalisa Ta Lissafo Manyan Zunuban da Suka Sanya aka Dakatar da Natasha

  • Majalisar dattawa ta fito ta kare kanta kan dakatarwar da ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya musanta cewa an dakatar da ita ne saboda yi zargin cin zarafi a kan Godswill Akpabio
  • Opeyemi Bamidele ya jero laifukan da Sanata Natasha ta yi waɗanda suka jawo aka dakatar da ita

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta musanta iƙirarin da ke yawo cewa an dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, saboda ta zargi Sanata Godswill Akpabio, da ci mata zarafi.

Majalisar ta bayyana cewa an dakatar da Natasha ne musamman saboda rashin biyayyarta ga sashe na 6.1 da 6.2 na dokokin majalisar da kuma halayenta na rashin ladabi a yayin zaman majalisar.

Majalisa ta kare matakin dakatar da Sanata Natasha
Majalisar dattawa ta dakatar da Natasha Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Akpabio ya kasa hakura, ya yi magana mai zafi kan zargin lalata da matar aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Bamidele ya bayyana cewa wasu kafafen yaɗa labarai na ƙoƙarin yaɗa bayanan ƙarya da gurbatattun labarai kan batun dakatar da Sanata Natasha.

Meyasa aka dakatar da Sanata Natasha?

Majalisar dattawa dai ta dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda zargin rashin ɗa’a da kin bin tsarin zaman majalisa.

Majalisar ta jaddada dakatarwar tare da sharaɗin cewa idan Natasha Akpoti-Uduaghan ta rubuta takardar neman afuwa, shugabannin majalisar na iya yin la’akari da ɗage dakatarwar kafin wa’adin watanni shida ya cika.

Sai dai, sanarwar ta ce maimakon bin ka’idojin majalisar, Sanata Natasha ta riƙa yaudarar jama’a da cewa an dakatar da ita ne saboda zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar dattawa, rahoton TheCable ya tabbatar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙorafin da Akpoti-Uduaghan ta gabatar kan cin zarafi bai cika sharuddan da aka gindaya ba na miƙa koke a gaban majalisar dattawa.

"Majalisa ta lura da yadda wasu rahotanni a kafafen yaɗa labarai ke ƙoƙarin nuna cewa an dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda zargin cin zarafi."

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fede gaskiya kan takaddamar Akpabio da Natasha

"Wannan batu ba gaskiya ba ne, yaudara ce, kuma ƙoƙari ne na karkatar da gaskiyar al’amarin. Idan Natasha Akpoti-Uduaghan ta bi ƙa’idojin da suka dace, majalisa za ta duba korafinta bisa cancanta da bin tsarin aiki."
"Amma ba ta bi ƙa'idojin da suka dace da wannan cibiyar ba wacce take aiki a ƙarƙashinta."

- Sanata Opeyemi Bamidele

Waɗanne laifuka Natasha ta yi?

Shugaban masu rinjayen na majalisar ya lissafo laifukan da suka sanya aka dakatar da Sanata Natasha Akpoti.

"Ta ƙi zaunawa a kujerarta da aka tanadar mata yayin zaman majalisa a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2025, duk da roƙon da shugaban marasa rinjaye da sauran manyan sanatoci suka yi, wannan kuwa rashin biyayya ne da rashin ɗa’a."
"Ta yi magana ba tare da samun izini daga shugaban majalisa ba, wanda hakan ya saɓawa ƙa’idojin majalisar a ranar 25 ga Fabrairu, 2025."
"Ta aikata abin da ya haifar da hayaniya da cikas ga zaman majalisa. Ta yi kalaman batanci da rashin girmamawa ga shugabannin majalisar."

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha, sun yi mata babban alkawari

- Sanata Opeyemi Bamidele

Akpabio ya magantu kan zargin Natasha

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan zarginsa da Sanata Natasha Akpoti ta yi kan cin zarafinta.

Godswill Akpabio ya bayyana cewa Natasha ba ta tashi zarginsa ba sai da ya sauya mata wurin zama da kwamitin da take shugabanta a majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng