Takardun Kotu Sun Nuna Yadda Tsohon Akanta Janar a Bauchi Ya 'Wawuri' N40bn

Takardun Kotu Sun Nuna Yadda Tsohon Akanta Janar a Bauchi Ya 'Wawuri' N40bn

  • Takardun kotu sun zargi tsohon Akanta Janar na Bauchi, Dakta Sa’idu Abubakar, da karkatar da kusan Naira biliyan 40 da sunan rance
  • Ana zarginsa da amfani da sunan Gwamnatin Bauchi wajen neman rance don kwangilolin babura da ake cewa ba a gani a ƙasa ba
  • Gwamnatin jihar ta shigar da tuhume-tuhume 16 da suka haɗa da zamba, ƙirƙirar takardun bogi, cin amanar aiki da karkatar da kuɗin talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Sababbin takardun da aka gabatar a Babbar Kotun Jihar Bauchi sun bayyana yadda ake zargin tsohon Akanta Janar na jihar, Dakta Sa’idu Abubakar rub da ciki a kan kuɗin jama'a.

Ana zargin ya karbo rance na biliyoyin Naira ta hanyar amfani da takardun amincewa na bogi tare da karkatar da kuɗain zuwa wasu kwangilolin samar da babura da ake cewa babu su.

Kara karanta wannan

Yadda miji da mata suka tafka damfarar kusan N2bn da matakin da EFCC ta dauka

An gano yadda tsohon Akanta Janar ya wawashe kudi a Bauchi
Tsohon Akanta Janar, Dakta Sa’idu Abubakar, Gwamna Bala AbdulKadir Mohammed Hoto: Daily Nigerian/Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Source: Facebook

Daily Nigerian ta wallafa cewa a cikin takardun ƙarar da gwamnatin Bauchi ta shigar, ana zargin Dakta Sa’idu da aikata laifuffukan zamba, yaudara da cin amanar aiki.

Zargin da ake yi wa tsohon jami'in Bauchi

The Guardian ta wallafa cewa ana zargin Dakta Sa’idu Abubakar ya yi amfani da takardun amincewar Majalisar Zartarwa ta Jiha, Majalisar Dokoki.

Ya samo takardun ISPO na bogi wajen samun rance daga bankunan UBA da Polaris a madadin gwamnatin Bauchi ba tare da sahalewar Gwamna Bala Mohammed ko Majalisar Zartarwa ba.

Ana zargin ya karkatar da rancen N3bn da aka ce an samo daga UBA domin kwangilar babura 5,000, sannan ya yaudari sakataren Majalisar Dokoki da Babban Sakataren gwamnati cewa an amince da rancen UBA.

Ana zargin dakta Sa’idu Abubakar ya yaudari bankuna da jami'an gwamnati
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana zargin ya karkatar da Naira biliyan 4.6 daga rancen bankin Polaris Bank domin sayen babura 15,000 da babu su, babu kamarsu.

Ana zargin ya karkatar da Naira biliyan 3.36 daga wani rancen UBA domin samar da babura 7,000 da gabatar da bayanan ƙarya cewa hukumomin da suka dace sun amince da wannan rance.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: DSS ta kai wanda ake zargi da zuga sojoji gaban kotu

Ana zargin ya ƙirƙiri takardar ISPO ta bogi domin biyan wannan rancen da aka ce ba bisa ka’ida aka samu ba.

Sauran tuhume-tuhumen da ake yi masa

Ana zargin ya yi amfani da takardun bogi wajen samun rancen Naira biliyan 4.65 daga Polaris Bank, sannan ya ƙirƙiri wata takardar ISPO ta bogi domin biyan rancen Polaris Bank.

Ana zargin ya yi amfani da takardun bogi wajen samun rancen Naira biliyan 3.36 daga UBA,ya kuma ƙirƙirar wata takardar ISPO ta bogi da ta shafi wannan rance na UBA.

Ana zargin ya mallaki takardun bogi da aka yi niyyar amfani da su wajen samun rancen N3bn daga UBA, kuma ya mallaki takardun bogi da suka taimaka wajen neman rancen Naira biliyan 4.65 daga Polaris Bank.

Ana zargin ya mallaki wasu takardun bogi da suka shafi rancen Naira biliyan 3.36 daga UBA, kuma ya ci amanar aiki ta hanyar samo rance ba bisa ka’ida ba daga Polaris Bank da UBA a madadin gwamnatin Bauchi.

Ana ci gaba da shari’ar a gaban Babbar Kotun Jihar Bauchi, yayin da gwamnatin jihar ke neman a hukunta tsohon Akanta Janar bisa laifuffukan da ake zargin ya aikata.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

An kama Akanta Janar a Bauchi

A baya, mun wallafa cewa jami’an EFCC sun cafke Akanta Janar na Bauchi, Sirajo Jaja, tare da wasu mutane biyu bisa zargin karkatar da N70bn a madadin gwamnatin jihar.

Ana zargin an cire Naira biliyan 59 daga asusun jihar, inda aka biya wakilan jam’iyya da abokan siyasar Gwamna Bala Mohammed da biliyoyin kuɗin jama'a da aka wawure.

Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, ya kuma bayyana halin da ake ciki a yanzu na daukar mataki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng