Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Fitar da Saƙo Mai Zafi bayan Dakatar da Ita a Majalisa

Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Fitar da Saƙo Mai Zafi bayan Dakatar da Ita a Majalisa

  • Sanata Cyril Fasuyi, mai wakiltar Ekiti ta Arewa ya yi ikirarin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta taɓa zargin Kayode Fayemi da cin zarafinta
  • Akpoti-Uduaghan ta mayar da martani, tana zargin Fasuyi da yi mata karya a zauren majalisa yayin da yake ambato ayoyin Littafi Mai Tsarki
  • Ta ce babu lokacin da ta taba zargin Fayemi da sayar da Kamfanin Karafa na Ajaokuta, ta yi Allah wadai da kokarin bata mata suna a bainar jama’a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta maidawa abokin aikinta, Sanata Cyrill Fasuryi martani.

Sanata Natasha ta zargi Sanata Cyril Fasuyi daga jihar Ekiti da jingina mata ƙarya a lokacin zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, 5 ga Maris, 2025.

Fayemi da Natasha.
Sanata Natasha ta yabi tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi Hoto: Natasha H. Akpoti, Kayode Fayemi
Asali: Facebook

Natasha wacce ke fuskantar hukunci kan zargin karya doka ta bayyana haka ne a wani gajeren saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Sanatan Katsina ya fusata, ya soki sharadin yi wa Natasha afuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha ta taɓa zargin Fayemi

Legit Hausa ta ruwaito cewa Sanata Fasuyi ya yi ikirarin cewa Natasha Akpoti-Uduaghan ta taba yin wasu kalamai marasa, tana zargin tsohon gwamnan Ekiti. Kayode Fayemi da cin zarafinta.

A cewarsa, Natasha ta zargi Fayemi ne a lokacin da yake rike da mukamin ministan ma’adanai da ci gaban karafa a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon ministan ya musanta zargin

Sai dai, a wata sanarwa da mai magana Fayemi, Ahmad Sajoh, ya fitar, tsohon gwamnan ya musanta zargin cewa Sanata Natasha ta ci zarafinsa.

Tsohon ministan ya ƙara da cewa duk wata hulda da ta shiga tsakaninsa da Natasha Akpoti-Uduaghan ta kasance ne a kan aiki kawai, ba tare da wata matsala ta kashin kai ba.

Sanata Natasha.
Sanata Natasha ya caccaki ɗan majalisa kan karyar da ya yi mata Hoto: Natasha H. Akpoti
Asali: Twitter

Sanata Natasha ta yabawa Fayemi

Da take mayar da martani kan bayanin Fayemi, Sanata Natasha ta wallafa wata gajeriyar sanarwa a shafinta na Facebook, inda ta yaba wa tsohon ministan bisa fitowa fili ya fadi gaskiya.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha ta sake yamutsa Hazo, ta yi magana kan dakatar da ita

Ta ce:

"Nagode, Mai Girma @kfayemi, saboda ka fito ka fadi gaskiya. Duk wani abu da na yi a wannan lokacin a matsayin minista ya kasance ne domin kokarin farfado da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta.
"Abin kunya ne ga Sanata Cyril Fasuyi ya fito yana faɗin karya a kaina kuma a zauren majalisa a daidai lokacin da yake ambato Littafi Mai Tsarki. Lallai, Allah mai hakuri ne."

Wannan sabuwar rigima na kara nuna yadda siyasar majalisar dattawa ke kara daukar sabon salo, musamman kan batutuwa da suka shafi shugabanci da rawar da sanatoci ke takawa a wakilcin al’ummarsu.

Majalisa ta dakatar da Sanata Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa bayan kai ruwa da rana, majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.

Majalisar ta kuma dakatar da albashi da alawus na Sanata Natasha, rufe ofishinta, janye jami’an tsaro, da hana ta zuwa ko kusa da majalisar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng